Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Manomi A Yankin Beji Ya Yabawa Gwamnati Kan Yunkurin Kawo Karshen ‘Yan Ta'adda

*Ba Mu Fahimci Tsarin Gwamnatin Jiha Na Shirin Noman Bana Ba Daga Awwal Umar Kontagora Wani manomi kuma makiyayi a yankin Beji ta karamar hu...


*Ba Mu Fahimci Tsarin Gwamnatin Jiha Na Shirin Noman Bana Ba

Daga Awwal Umar Kontagora

Wani manomi kuma makiyayi a yankin Beji ta karamar hukumar Bosso a jihar Neja, Malam Abdullahi Mu'azu Beji ya yabawa gwamnatin jiha da jami'an tsaro kan yunkurin kawo karshen yan ta'adda masu garkuwa da jama'a da suka hana manoma yin noma yadda ya kamata a shekarar da ta gabata, ya ce wannan yunkurin na gwamnati abin a yaba ne domin yau kusan watanni uku ke nan ba su ji labarin 'yan ta'addar ba balle wani garkuwa da wani talaka a yankin nan.

"Idan hakan ya dore muna da tabbacin a damanar bana manoma za su koma daji, sai dai abin da ba mu fahimta ba, shi ne yadda gwamnati ta share gonakin mu, wanda mu dai iyayen mu na kasar Beji sama da shekaru sittin zuwa sama, a nan aka haifi iyayen mu, mu kan mu hayayyafa kuma mun aurar, wadannan gonakin na mu da ya shafi Gwarawa da Fulani a nan muke kiwo kuma muke noma, yau an share gonakin tare da sare Itacen da muka tashi muka gan su da iyakokin gonakin mu" in ji shi. 

Ya ci gaba da cewa; "Mu dai gwamnati ba tace mana komai ba, yayin wannan aikin kuma mun ji an ce mu ne zamu noma wurin, to ba mu san tsarin da aka yi ba, kuma gwamnati ba tace mana komai ba, sannan ba wani Basarake a yankin nan da ya yi muna karin haske kan wannan lamarin, shi yasa na ke jawo hankalin wadanda abin ya shafa a zauna a yi tsari tunda wuri kafin lokaci ya kure, dan jama'a sun damu gaya da wannan tsarin da aka zo mana da shi rana tsaka".

"Manoman Beji, ba wannan ne damuwarsu ba, misali ni da ke magana yanzu haka na tanadi irin doya, shinkafa da masara da na saba nomawa, abin da muke bukata shi ne taki, idan gwamnati ta samar mana da takin zamani kan lokaci zai fi amfanuwa akan wannan tsarin da ba mu san yadda yake ba.

"Saboda haka, muna kira ga adali gwamna, kuma Manomi Umar Bago da ya yi kyakkyawar bincike ya san abin da ake son yi wa manoman Beji ba su amince da shi ba, wannan dai gonakin mu ne ba saura ne da ba kowa akan sa ba, ya kamata kowani manomi ya san iyakacin gonarsa, idan ma wani tallafin za a ba mu a shawarce mu kafin fuskantar aikin gadan-gadan", ya jaddada.

Amb. Nura Hashim, shi ne mataimakin shugaban kungiyar manoma ta jiha (AFAN), ya ce ba gwamnati na yunkurin karbe gonakin manoma ba ne, wani sabon tsarin noma ne na zamani da za a taimakawa manomi ta yadda za ci amfanin abin da yake nomawa, ta hanyar bashi rance da karfafa guiwar sa akan aikin noma.

Duk masu tsoron kwace gonarsu su yi hakuri ba haka tsarin yake ba, yanzu gwamnatin jiha ta samar da dukkan wani abin da manomi ke bukata na aikin noma, kuma a tsarin na bana saboda tsaro Sarakunan gargajiya da kungiyoyin manoma na yankunan za a tabbatar an sanya su dan samun sauki ababen da aka rantawa manoman.

Kasar Beji dai a baya ta fama da matsalolin tsaro na 'yan ta'adda masu garkuwa da jama'a da ya kai ga rarrabuwan kawunan kabilu mazauna yankin bisa zargin juna da yin cin ne, tun bayan zuwan gwamnatin nan ta himmantu wajen tsalkake yankunan da yan ta'addan suka samu matsugunni da ceto tattalin arzikin yankin da rayukan jama'a da ke salwanta a kowani lokaci. 


No comments