Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Buɗe Taron Karawa Juna Sani Na Ƙasa Kan Bunƙasa Kimiyyar Karatu Daga Nesa

  Daga Idris Umar, Zariya An buɗe taron ƙarawa juna sani kan buƙasa kimiyyar karatu daga nesa a harabar ilmi baki ɗaya. Taron an gudanar da ...

 

Daga Idris Umar, Zariya

An buɗe taron ƙarawa juna sani kan buƙasa kimiyyar karatu daga nesa a harabar ilmi baki ɗaya.

Taron an gudanar da shi ne a babban ɗakin taro na jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya (Assembly hall).

Manyan mutane sun gabatar da mukaloli da dama da suke kira akan bunƙasa harkar kimiyyar karatu daga nesa tare da kawo amfaninsa ga al'ummar ƙasa baki da kuma sun kawa ƙalubalen dake cikinsa.

Daga cikin manyan baƙin da suka sami halartar wannan taro aƙwai wakilin babban Sakataren NUC Mista  Chris J. Mai Yaki, akwai wakilin Mukaddashin jami'ar Ahmadu Bello Zariya Farfesa Ahmed Dako Ibrahim akwai  Hajiya Rakiya Gambo Iliyasu Darakta daga UEF da sauran manyan baƙi daga ƙasashen ƙetare

Bayan ƙammala ƙaddamar da bude tarone, shugaban ƙwamitin taron kuma shugaban tsangayar Distance Learning na Ahmad Bello Zaria Farfesa Ibrahim Sule ya yi wa manema labarai karin haske dangane da taron. 


No comments