Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kwamitin Da Aka Kafa Don Bincikar Gwamnatin Ganduje Ya Fara Aiki

  Kwamitin bincike da gwamnatin Kano ta kafa domin binciken batun zargin wadaÆ™a da dukiyar al'umma ya fara zamansa na farko. Kwamitin za...

 


Kwamitin bincike da gwamnatin Kano ta kafa domin binciken batun zargin wadaƙa da dukiyar al'umma ya fara zamansa na farko.

Kwamitin zai yi bincike ne tsakanin 2015 da 2023, wato zamanin mulkin, Dr Abdullahi Umar Ganduje, inda ake fatan kwamitin zai karÉ“i Æ™orafe-Æ™orafe daga jama’a da kuma ‘yan Æ™ungiyoyi a kan yadda tsohon gwamnan ya yi tasarrufi da kadarorin gwamnati.

A kwanakin baya ne gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya kafa kwamatocin bincike biyu da za su binciki zargin al’mundahana da rikicin siyasa da É“atan mutane a jihar, al’amarin da ya haifar da zazzafar muhawara.

Kwamitin binciken Æ™arkashin jagorancin mai shari’a Faruk Lawan Adamu, ya ce al'umma suna da damar zuwa kwamitin, su gabatar da duk wani Æ™orafi ko rashin gamsuwa da yadda aka tafiyar da gwamnatin jihar Kano daga 2015 zuwa 2023.

Barista Bashir Sale mamba ne a kwamitin binciken kuma ya yi wa BBC ƙarin bayani game da farko da kwamitin ya yi.

Ya ce "kadarorin gwamnati - makarantu da filaye da gidaje, maƙabartu da burtali, ya ya aka yi da su? An sayar? bisa ƙa'ida aka sayar? Idan ba bisa ƙa'ida aka sayar ba, wa ya siya, idan kuma ka siya, wa ka siyarwa?

Ya kuma ce za su bi ƙa'ida da yin adalci a binciken da za su yi.

Nan gaba ne kuma za a fara sauraron bahasi daga É“angarori daban-daban ciki har da duk wanda yake ji an aiwatar da wani aiki a yankinsa da bai gamsu da shi ba.

Akwai kuma kwamitin da zai yi bincike a kan rikice-riciken siyasa da mutanen da suka É“ata da tashin hankalin da aka yi a 2015 da 2019 da kuma 2023.

Kafa wannan kwamatocin bincike dai ya haifar da ce-ce-ku-ce da kace-na-ce tsakanin ɓangaren tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da kuma gwamnatin NNPP, inda bangaren Gandujen ke zargin akwai bita-da-ƙulli a binciken da ake ƙoƙarin yi, kasancewar an zaɓi tsohon gwamna ɗaya ne wajen yin binciken, zargin da gwamnatin kwankwasiyya ta musanta.

No comments