Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Tinubu Na Jimamin Mutuwar Mutane A Fashewar Tankar Mai A Rivers

Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan mutanen da suka mutu sakamakon tashin gobara a wata tankar mai a Pat...



Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan mutanen da suka mutu sakamakon tashin gobara a wata tankar mai a Patakwal da ke jihar Rivers.

Cikin wata sanarwa da kakakinsa, Ajuri Ngelale ya fitar ranar Lahadi, shugaba Tnubu ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga gwamnati da al'ummar jihar Rivers game da ibtila'in da ya faru har mutane da dama suka rasa rayukansu baya ga asarar dukiya.

Shugaba Tinubu ya yi addu'ar samun sauƙi ga waɗanda suka ji rauni sakamakon lamarin.

Shugaban ya umarci hukumomin gwamnati a jihar su ci gaba da aiki da gwamnati domin samar wa mutanen da lamarin ya ritsa da su tallafi.

Shugaba Tinubu ya yaba wa jami'an da suka yi gaggawar agazawa mutanen da suka gamu da ibtila'in .

Ita ma uwargidan shugaban Najeriya, Oluremi Tinubu ta miƙa saƙon ta'aziyyarta ga gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara da iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a fashewar tankar man.

No comments