Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sojoji Sun Tarwatsa Maɓoyar Ƴanbindiga, Sun Kuɓutar Da Mutane A Taraba

Dakarun Najeriya da ke aiki ƙarƙashin rundunar murƙushe ayyukan ƴanbindiga a jihar Taraba ta Whirl Stroke sun tarwatsa wani sansanin ƴanbind...



Dakarun Najeriya da ke aiki ƙarƙashin rundunar murƙushe ayyukan ƴanbindiga a jihar Taraba ta Whirl Stroke sun tarwatsa wani sansanin ƴanbindiga inda suka kuɓutar da mutanen da aka yi garkuwa da su tare da gano tarin makamai da alburusai.

Rundunar sojin Najeriyar ce ta wallafa hakan cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X.

A cewar sanarwar, dakarun da aka girke a Fikyu, a ranar 29 ga watan Afrilu sun kai ɗauki kan wasu rahotanni da suka samu cewa wasu da ake zargi ƴanbindiga ne sun buɗe wuta a yankin Pukun da ke Fikyu a ƙaramar hukumar Ussa. Sojojin sun yi musayar wuta da su har suka samu galaba a kansu.

Ƙarin binciken a yankin ya sa sojoji sun gano bindiga ƙirar AK47 da ƙunshin alburusai.

Kazalika, sojojin da aka tura Kufai Amadu da Kasuwan Haske tare da haɗin gwiwar sojoji daga runduna ta ɗaya sun ɗauki mataki kan wani bayanin sirri da suka samu game da maɓoyar ƴanbindiga a ƙauyen Vingir da ke ƙaramar hukumar Katsina Ala a jihar Benue. A nan ma sojojin sun yi arangama da ɓatagarin inda suka murƙushe su.

Sojoji sun kama wani da ake zargi mai garkuwa da mutane ne da aka same shi da wayoyin hannu biyu ƙirar Techno da kuɗi naira dubu 40.

An yi bincike a sansaninsu inda kuma aka gano bindiga ƙirar AK47 sannan aka samu kuɓutar da Dakta James Raphael da ɗansa a Gbeji a ƙaramar hukumar Ukum da ke jihar Benue.

Sanarwar ta kuma ce sojojin da ke aiki a bataliya ta 20 sun kama wani mutum a ƙaramar hukumar Bali da ke jihar Taraba tare da buhu huɗu na wani abu da ake tunanin tabar wiwi ce.

Rundunar ta ce mutumin ya daɗe ana neman shi ruwa a jallo saboda yadda yake ta'amali da miyagun ƙwayoyi da kuma samar wa ƴan bindiga da sauran masu laifi miyagun ƙwayoyi.

No comments