Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Bai Wa Gwamna Bago Makullin Dakin Ka'aba Karramawa Ce Ga Jihar Neja - Masha'Allahu

Daga Awwal Umar Kontagora An bayyana baiwa manomi gwamnan Umaru Mohammed Bago makullin Ka'aba da hukumomin Saudiya suka yi karramawa ce ...


Daga Awwal Umar Kontagora

An bayyana baiwa manomi gwamnan Umaru Mohammed Bago makullin Ka'aba da hukumomin Saudiya suka yi karramawa ce ga jihar Neja, wannan ya samo asali a tarihin musulunci a samu natijajjan mutum da yake yi wa addini hidima dan bude dakin ka'aba a lokacin aikin hajji.

Sheikh Muhammadu Liman ( Masha'Allahu) shugaban kungiyar horar da maniyyata aikin hajji da umrah a jihar Neja shi ya bayyana hakan ga wakilin mu.

Malamin ya cigaba da cewar wannan karramawa ce mafi daraja da ya kamata mu yi alfahari da shi sabanin duk wata karramawar da gwamna zai samu a duniya.

Masu tsegumin cewar gwamna yayi anfani da kudaden da ya kamata ya yiwa al'ummar Neja aiki da su, a matsayin soki burutsu, domin kasar Saudiya ta wuce mutum yace sai an bada rashawa kafin ta karrama mutum duba da irin tattalin arzikin kasar da hidimar da ta ke yiwa kasashen musulmi a duniya.

Ya kamata jama'a su sani bada shaidar da mutum zai yi, ya bada shaidar abinda kwakwalwa za ta yarda da shi. Allah ya ma bayyana mana cewar mutum ya daina yayata abinda baya da ilimi akan shi, saboda haka mutane su daina bada shaidar abinda ba su da ilimi akan shi, mu dauki wannan karramawar da muhimmanci domin karramawa ce gare al'ummar jihar nan, duba da irin karamcin da muka samu na yin tsayin daka wajen daukaka addinin musulunci a idanun kasashen musulmi.

Liman Masha'allahu, ya cigaba da cewar wannan na nufin maniyyatan jihar Neja a bana zasu samu kulawa ta musamman ga hukumomin kasar Saudiya a lokacin wannan aikin hajjin mai zuwa, domin muna kyautata cewar manomi gwamna Umar Bago shi zai bude ka'aba a hajjin bana.

Liman ya jawo hankalin maniyyatan bana da su zama masu bin doka da oda a kasa mai tsalki, su tabbatar sun zamo maniyyatan da za a cigaba da yin misali da su ko bayan kammala aikin hajjin.

Da ya juya kan zargin da ake yiwa maniyyata na tsallakawa kasar saudiya da kayan da aka haramta kuwa, yace a bana an zo da sabbin tsare tsare, duk maniyyacin da ya bari aka kama shi ya tabbatar zai dandana hukunci kuma ya zamo daya daga cikin maciya amanar kasa.

Malamin, yace yanzu haka duk wasu tsare tsaren da aka fitar mun shirya da hukumar jin dadin alhazai ta jiha dan wayar da kan maniyyatan da za su tashi daga jihar nan, daga alhamis biyu ga watan maris kungiyar mu za ta kaddamar da fara horar da maniyyata a hukumar jin dadin alhazai ta jiha kafin sauran kananan hukumomi ashirin da biyar su cigaba a cibiyoyin da muka tanada a yankunan kananan hukumomin jihar. 

No comments