Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Hajji Da Umrah Trainers Ita Ce Kungiyar Da Tafi Kowacce Jajircewa Wajen Horar Da Maniyyata - Wakilin Malaman Nupe

Daga Awwal Umar Kontagora An bayyana cewar kungiyar Hajji and Umrah Trainers ta jihar Neja karkashin jagorancin Sheikh Muhammad Lawal (Masha...



Daga Awwal Umar Kontagora

An bayyana cewar kungiyar Hajji and Umrah Trainers ta jihar Neja karkashin jagorancin Sheikh Muhammad Lawal (Masha'Allahu) ita ce kungiyar da tafi kowacce kungiya jajircewa wajen horar da maniiyyata da jihar Neja, babban daraktan hukumar kula da harkkokin addinai ta jihar, Sheikh Umar Faruk Abdallah ne ya bayyana hakan a lokacin kaddamar shirin horar da maniyyatan bana a dakin taro na hukumar jindadin alhazai ta jiha.

Umar Faruk, ya jawo hankalin kungiyar da ta hada kai da hukumar dan sanin sabbin tsare tsaaren kasar Saudiya akan yadda ayyukan hajjin bana zai kkasance, domin mun samu labarin akwai tsare tsaren da kasar ta gabatarwa kasashen duniya.

Da yake kaddamar da fara shirin horarwar, darakta mai kula da ayyukan hukumar, Sheikh Attahiru Bala Dukku, wanda ya wakilci babban sakataren hukumar Malam Awwal Aliyu yayi karin haske kan kudaden da za a baiwa maniyyata a matsayin kudin guzuri, inda yace zai kasance dala dari biyar wanda yayi daidaii da darajar riyal dubu da dari takwas da hamsin.

Dukku, ya cigaba da cewar wannan aikin da wadannan kungiyoyi ke yi aikin hukumarsu, amma da yake aikin hidimtawa addini ne yasa a kowani lokaci hukumarmu ke karfafa guiwarsu. Dan haka kamar yadda na bayyana masu zan isar da bukatunsu ga sakataren hukumar dan ganin an ba su gudunmawar da ayyukan su zai cigaba da dorewa.

An samu sauye sauye da dama daga kasar Saudiya tun daga kan kudin kujera inda aka farko an shelanta biyan milliyan hudu da dubu dari biya wanda zuwa yanzu wasu sun cika wa'adin wasu kuma abin bai yiwu ba.

Jihar Neja dai a bana tana da maniyyata dubu uku da ashirin da hudu, wadanda sun cika dukkanin ka'idodin da aka bayyana.

Saboda haka daga yau hukumar jin dadin alhazai ta bude cigaba da horar da maniyyata a dukkanin yankunan kananan hukumomi ashirin da biyar.

Da yake bayani bayan kadddamarwar, shugaban kungiyar Niiger State Hajji and Umrah Trainers Association, na jihar Neja. Sheikh Muhammad Lawal ( Masha'Allahu), yace yau sun kaddamar da abu biyu, bude taron wayar da kan maniyyata a jihar Neja da yiwa kasa da gwamnan Neja addu'o'in musamman.

Mun gayyaci malamai na kananan hukumomi ashirin da biyar dan jin sabbin tsare tsaren hukumar jin dadin alhazai, wanda kasar Saudiya ta gabatarwa kasashen duniya, domin idan sun koma kananan hukumominsu su san abinda zasu bayyanawa jama'a a cibiiyoyin horarwa.

Bayan nan mun shirya addu'o'in musamman ga kasa da gwamnatin jihar Neja, musamman iriin namijin kokarin da gwamnatocin ke yi amma yanayin da ake ciki, yasa dole mu fadawa Allah, domin samun nasarar su itace nasarar al'ummar jihar Neja.

Shugaban ya jawo hankalin malamai da su jajirce fiye da yadda suke yi a baya, kuma kungiya za ta tabbatar duk wani sabon abinda ba san da shi ba daga hukumomin Saudiya inda yazo mana za mu sanar da su.

Hukumar dai ta bayyana cewar aikin hajjin bana ba zai wuce kwanaki talatin da biyar ba kamar yadda hukumomin Saudiya ta bayyana. 

No comments