Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Joshua Azumi Bawa Ya Zama Ɗan Takarar ADC Bayan Sahihin Zaɓen Fidda Gwani Na Mazabar Munya

Daga Awwal Umar Kontagora Jam'iyyar ADC a jihar Neja ta tabbatar da Hon. Joshua Azimi Bawa a matsayin dan takarar da lashe z...

Daga Awwal Umar Kontagora

Jam'iyyar ADC a jihar Neja ta tabbatar da Hon. Joshua Azimi Bawa a matsayin dan takarar da lashe zaben cike gurbi na majalisar dokokin jihar Neja wanda zai wakilci karamar hukumar Munya, da za a gudanar da zaben cikin watan Agusta mai kamawa. Shugaban jam'iyyar, Alhaji Musa Hassan ne ya tabbatar da hakan a wani hira da manema labarai.
Shugaban ADC din ya cigaba da cewar hudu ga wata mai fita ne hukumar zabe ta tsayar ranar fara yakin neman zabe, dan haka ya umurci yayan jam'iyyar da su gudanar da yakin neman zaben cikin lumana dan samun nasarar zaben.

Da ya juya kan yan hadaka kuwa, yace har yanzu kofa a bude take ga dukkan mai sha'awar shigowa jam'iyyar, amma ba daidai ba ne wasu su yi kungiya kuma suna anfani da tambarin jam'iyya alhalin jam'iyya ba ta san da zaman su ba.

Duk wani dan siyasa da ke wata jam'iyya kuma yake sha'awar shigowa jam'iyyar mu kofa a bude take kuma a kowani lokaci muna maraba da su, su zo mu tattauna dan samun mafitar yadda za mu hada hannu dan ceto kasar nan da jihar Neja daga halin da muka samu kan mu.

Saboda haka, duk wani dan ADC mace ko matashi da masu fada aji da su yan hadaka su marawa Hon. Joshua Azimi Bawa shi ne dan takarar da ya samu nasarar lashe zaben fidda gwani, dan fuskantar wannan zaben cike gurbin na majalisar dokokin jihar Neja.

"Ba ni da kuri'a a karamar hukumar Munya, su yan karamar hukumar ne ke da katin zabe a wannan karamar hukumar kuma marawa ADC baya dan ganin samun wannan nasarar zaben shi ne zai ba mu kwarin guiwa a manyan zabuka na gaba.
Alhaji Hassan, yace ba kin kowa duk wanda ke da rawar takawa dan samun nasarar ADC muna maraba da shi, amma su sani cewar ADC daya ce, kuma ni ne shugabanta a jihar Neja. Amma abinda su ke yi da tambarin jam'iyyar ADC suna kara daga jam'iyyar ne da kara ma ta kwarjini a wajen jama'a, wanda yasa muna kara samun karbuwa da kwarin guiwar shigowarsu a cikin jam'iyya in har sun yi abinda ya dace za mu samu gagarumin nasara a dukkanin zabukan da za mu fuskanta.

No comments