Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Illolin Mulkin Buhari daga 2015 zuwa 2023

Rubutun Abdulaziz T. Bako   Bayan shekaru 8 na mulkin Buhari, ga yadda Najeriya ta Æ™ara tsunduma cikin matsaloli da tabarbarewar...


Rubutun Abdulaziz T. Bako 

Bayan shekaru 8 na mulkin Buhari, ga yadda Najeriya ta ƙara tsunduma cikin matsaloli da tabarbarewar rayuwa a fannoni daban-daban. Wannan bayani yana kunshe da hujjoji, sahihan lambobin ƙididdiga, da misalai daga rahotanni na hukumomi da masana tattalin arziki.

🇳🇬 Illolin da suka shafi Najeriya gaba ɗaya:

1️⃣ Tattalin Arziki Ya Lalace:
Najeriya ta shiga cikin karayar tattalin arziki (recession) sau biyu a mulkinsa – 2016 da 2020. GDP ya ragu daga $594bn (2015) zuwa $460bn (2023).

2️⃣ Tsadar Rayuwa Ta Tashi:
Hauhawar farashin kaya (inflation) ya tashi daga 8.7% a 2015 zuwa fiye da 22% a 2023. Naira ta karye daga ₦197 duk dala zuwa ₦465/$ (a hukumance), ko ₦740/$ a kasuwa.

3️⃣ Rashin Aiki Ya Karu:
Adadin marasa aikin yi ya tashi daga 7.5% zuwa fiye da 33.3% a 2023. Ma'ana idan ka tara mutum 100 kafin Buhari ya hau mulki mutum 7 zuwa 8 ne kacal za ka samu ba su da aikin yi. Amma bayan ya sauka a cikin mutum 100 mutum 33 ne basu da aiki. A takaice Buhari ya ninka adadin marasa aikin sau kusan biyar.

4️⃣ Bashin Ƙasa Ya Ƙaru:
Lokacin da Buhari ya hau ya tarar adadin bashin da a ke bin Najeriya bai wuce Naira Triliyan 12 ba, amma kafin ya sauka sai da wannan adadin ya ninka kansa sau 6 da É—oriya zuwa Naira triloyan 77. 

Haka a ka riÆ™a karya dokar Æ™asa a na cirar kuÉ—i daga CBN ba bisa Æ™aida ba ta hanyar “Ways and Means”. A Æ™a'idar wannan tsari bai kamata a É—auka daga CBN bai kamata ya kai Naira triliyan 1 ba, amma haka a ka riÆ™a karya dokar Æ™asa sai da aka Æ™wamushe sama da Naira triliyan 23 a kan idon Buhari. Abin takaicin ma shi ne bincike da gwamnatin tarayya ta sa aka yi a kwanan nan ya nuna cewa Naira triliya 17 a cikin wannan adadi na triliyan 23 ba a san inda ta shiga. Ta yi É“atan dabo (dukkan alamu suna nuna cewa sace kuÉ—in makusanta da muÆ™arraban Buhari suka yi).

Wannan adadin kuÉ—i da zaa rabawa Æ´an Najeriya shi yaro da babba kowa zai samu kimanin Naira dubu 80. 

Wannan kuɗi sun kusa biyu bisa uku na gaba ɗaya kudin da aka kasaftawa Najeriya a 2024 (har da wanda ɓarayi zasu sata da wanda zaa biya ma'aikata a yi ayyukan tafiyar da gwamnati. Amma wasu tsirarun mutane sun sace.

5️⃣ Fitar Mai Ta Ragu:
Adadin ɗanyen mai da a ke fitarwa ya ragu dga ganga miliyan 2.2 zuwa miliyan 1.1 a rana (ya koma rabin yadda a ke fitarwa). Kuma ɗaya daga cikin manyan maƙasudan dalilan da suka sanya hakan shi ne satar man da muƙarraban gwamnati suke yi suna karkatar da akalar man. Su saka kuɗin a aljihunsu.

Wani bincike ya nuna cewa a irin wannan an saci mai da yawansa ya kai kimanin Dollar biliyan 21.6, wanda idan ka juya shi zuwa Naira ya wuce Naira triliyan 31. Wannan adadi ya wuce yawan adadin kudin da zaa kasaftawa Najeriya baki É—ayanta (da wanda zaa sata da wanda zaa yi aiki da shi). In da zaa rabawa kowane É—an Najeriya wannan kuÉ—i kowa zai samu kimanin Naira dubu 150.

Bincike ya nuna cewa a ƙalla and saci kuɗi a ƙarƙashin mulkin Buhari sun wuce kimanin Naira Triliyan 55. Wannan kuɗi sun kasafin kuɗin Najeriya na shekara 2. Sannan da zaa raba kowane ɗan Najeriya wannan kuɗi kowa (yaro da babba) zai samu kimanin Naira dubu ɗari biyu da hamsin.

6️⃣ Talauci Ya Karu:
Mutane miliyan 133 na rayuwa cikin matsanancin talauci. Najeriya ta zama cibiyar talauci ta duniya a zamanin Buhari.

7️⃣ Masana’antu Sun DurÆ™ushe:
Rashin wutar lantarki da tsaro ya hana cigaban masana’antu. Jimillar kudin kasuwa (M2) ta tashi daga ₦15.35tn (2012) zuwa ₦52tn (2022) ba tare da ci gaba ba.

8️⃣ Wutar Lantarki Na Yawan Yanke:
National grid ya karye fiye da sau 200. Lamarin wutar lantarki ya taɓarɓare. Kuma na san mai karatu yana sane da irin kuɗaɗen da aka ce an kashe a kan tashar wuta ta Mambila a zamanin Buhari, amma a ka yi bincike a ka ga babu aikin komai da aka yi a wurin.

9️⃣ Rashin Tsaro:
Boko Haram, ‘yan bindiga da rikicin manoma da makiyaya sun kashe dubban mutane, sun kore miliyoyi daga gidajensu, sun sace dubban mutane, sun karbi triliyoyi a hannun mutane na kudin fansa.

🔟 Take Hakkin Dan Adam:

Ana zargin jami'an tsaro da kashe mabiya IMN (Shi’a) fiye da 300 zuwa 1000 a Zaria 2015

A lokacin #EndSARS, an kashe fiye da mutane 12 a Lekki Toll Gate

Haka zalika, mabiya IPOB a kudu maso gabas an sha kashe su bisa zalunci.

An kashe masu safarar shinkafa a board Nijet babu adadi

1️⃣1️⃣ Cin Hanci da Rashawa:
EFCC ta gaza aiki yadda ya kamata. NDDC ta yi asarar fiye da ₦6 trillion; ayyuka 13,000 sun tsaya cak. Buhari ya yafewa É“arayin gwamnati da kotu ta kulle, shi kuma ya sake su.

1️⃣2️⃣ Ilimi da Lafiya Sun Durkushe:

ASUU ta yi yajin aiki fiye da wata 13. Saboda zalunci an hana malaman makaranta albashi na wata da watanni

Yara miliyan 10.5 ba sa zuwa makaranta.

Kasafin lafiyar bai kai 5% ba. Asibitoci Sun sha fama da rashin ma’aikata da kayan aiki. Lokitoci sun da guduwa suna barin Æ™asa saboda rugujewar tattalin arziki

🕌 Illolin da suka fi shafar Arewacin Najeriya:

1️⃣ Yawaitar ‘Yan Bindiga da Garkuwa da Mutane:
Ƴan ta'adda sun ci karensu babu babbaka. Sun kashe dubban mutane tare, sun tashi garuruwa daban-daban, sun vi zarafin mata, sun hana noma a Zamfara Sokoto da Katsina. 

Ayyukan Soji Sun Gaza:
Duk da shiryen kamar Harbin Kunama da Sharan Daji, hare-haren ‘yan bindiga sun cigaba da tsananta.

2️⃣ Harin Masallatai da Kisan Manoma:
A Neja, an kashe É—aruruwan manoma.

3️⃣ Yan Gudun Hijira Sun Karu:
Fiye da 247,000 sun rasa matsuguni a Arewa maso Yamma. 77,000 sun tsere zuwa Jamhuriyar Nijar.

4️⃣ Rikicin Manoma da Makiyaya:
A Filato da Benue, rikicin ya kashe É—aruruwan mutane.

5️⃣ Boko Haram:
Har Buhari ya sauka Boko Haram sun ci gaba da kai hare-hare a Borno, Yobe da Adamawa. 

6️⃣ Hanyoyin Sufuri Sun Lalace:
Harin hanya Abuja–Kaduna da satar fasinjoji ya hana zirga-zirga da saka jari a Arewa.

7️⃣ Rashin Abinci da Magani a Sansanonin 'Yan Gudun Hijira:
Fiye da sansanoni 100 ba sa da ruwa mai tsafta ko kulawar lafiya.

8️⃣ An rufe makarantu:
Satar dalibai da hare-hare sun tilasta rufe makarantu da dama a Zamfara, Katsina da Borno.

Waɗannan su ne kaɗan daga cikin ɓarnar da aka yi a mulkin Buhari da a ke cewa dole sai mun yafe.

No comments