BBC Hausa ta labarto cewa; an harbe wani babban malamin addinin Musulunci a gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo. An yi wa Sheikh ...
BBC Hausa ta labarto cewa; an harbe wani babban malamin addinin Musulunci a gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.
An
yi wa Sheikh Ali Amini, ruwan albarussai yayin da yake jagorantar sallar Asham
a ranar Asabar a cikin babban masallacin garin Beni.
Har
yanzu dai ba a bayyana waÉ—anda suka aikata kisan ba.
Tun
da farko wasu da ake zargin ‘yan tawayen ADF ne sun kai hari kan wasu Æ™auyuka
biyu a yankin.
Rahotannin
da ba a tabbatar da su ba sun ce an kashe mutane 19 ciki har da sojoji da dama.
Yayin
da ƴan ƙasar ke ƙara fusata kan yawaitar hare-haren ƴan tawaye, shugaban kasar
Felix Tshisekedi a ranar Juma'a ya ayyana wani mataki na yi wa lardunan
Arewacin Kivu da Ituri ƙawanya- matakin da ake ganin zai bai wa sojojin Congo
karin karfi da ƙwarin gwiwa.
No comments