Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaro sun kama shugaban al’ummar Falasdinawa da ke zaune a Nijeriya, Abu Ramzi Ibrahim, a garin Abuja. La...
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaro sun kama shugaban al’ummar Falasdinawa da ke zaune a Nijeriya, Abu Ramzi Ibrahim, a garin Abuja. Lamarin dai ya faru ne a ranar Juma’a, 22 ga watan Agusta, 2025, kuma har zuwa safiyar Litinin, yana nan tsare.
Abu Ramzi, wanda ya shahara a matsayin ɗan Falasdinu kuma mazaunin Nijeriya, ya shafe shekaru da dama yana rayuwa a ƙasar, kuma rahotanni na cewa ya yi karatu a wata jami’a a Nijeriya. Ya shahara wajen fafutukar kare al’ummar Falasdinu da kuma bayyana ra’ayoyinsa a kafafen yaɗa labarai.
Bisa bayanan farko daga wasu da ke kusa da al’ummar Falasdinawan, har yanzu ba a bayyana dalilan kama shi ba. Ƙoƙarin da aka yi don jin ta bakin Jakadan Falasdinu a Nijeriya bai kai ga nasara ba har yanzu.
“Ya zama dole wannan abu ya fito fili. Dole ne mu san dalilin da ya sa aka kama shi kuma mu tabbatar da cewa yana cikin ƙoshin lafiya,” in ji wata majiya da ta san lamarin, wacce ta buƙaci a fara ɗaukar matakan wayar da kai da kuma sanya matsin lamba ta kafafen yaɗa labarai.
Ana kira ga ’yan jarida da kuma masu kare haƙƙin ɗan adam a faɗin ƙasar da su bibiyi wannan lamari, duba da irin gagarumar rawar da Abu Ramzi ke takawa wajen goyon bayan Falasdinu ta kafafen yaɗa labarai na Nijeriya.
Har zuwa lokacin da ake kammala wannan rahoto, babu wani bayani daga hukumomin Nijeriya da ke tabbatar da kama shi ko bayyana tuhumar da ake masa.
No comments