Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

'Yan Siyasar Neja Ta Arewa Su Yi Koyi Da Salon Wakilcin Sanata Lolo

Daga Awwal Umar Kontagora An nemi yan siyasan yankin Neja ta arewa da su yi koyi da salon wakilcin sanata mai wakiltar yankin, S...

Daga Awwal Umar Kontagora

An nemi yan siyasan yankin Neja ta arewa da su yi koyi da salon wakilcin sanata mai wakiltar yankin, Sanata Abubakar Sani Bello ( Lolo) wajen bada tallafi da sauraren jama'a ba tare da nuna bambanci ba. Wani jigon siyasa a yankin, Alhaji Muhammadu Lawal Ibrahim ( Hamdala) ne yayi kiran bayan bada tallafi ga al'ummar yankin da sanatan yayi a makon nan mai karewa. 

Hamdala, ya cigaba da cewar tabbas kasancewa Sanata Lolo a majalisar dattawa abin a yaba ne, domin irin wakilcin da ake nema ke nan, ta yadda kowani dan siyasa zai bar kofarsa a bude wajen sauraren jama'ar da yake wakilta da kokarin samar masu abubuwan morewa rayuwa ba tare da jiran komai sai gwamnatin jiha tayi ba, hakan abin a yaba ne da karfafa guiwa.

Tun bayan barin majalisar dattijai da marigayi Sanata Ibrahim Musa, ba mu samu sanata mai sauraren jama'a ba tare da nuna bambanci ba, ko nuna rashin alfanun jama'ar da yake wakilta ba, kowani lokaci ka bukaci ganin Sanata Lolo kofarsa a bude take kuma zai saurare ka, hakan yasa har mutanen da sa yankin da yake wakilta muddin daga jihar Neja ka fito zai saurare sakamakon kujerar gwamnan jihar da ya taba rikewa tsawon shekaru takwas.

Dan siyasar, ya shawarci Sanatan da ya kara kaimi wajen tallafawa mata da matasa ganin iron rawar da suke takawa lokacin zabe, muna bukatar karin kaimi wajen bada tallafin kiwon lafiya, bada tallafin karatu ga yayan marasa galihu da kuma karfafa guiwar iyaye mata da matasa a sana'o'in dogaro da kai.
Na yi fama da matsalar cutar mutuwar barin jiki, Sanata Abubakar Sani Bello ne ya dauki nauyin jinya ta kuma ire-iren mu na nan da dama, dan haka ina jawo hankalin makusantar shi da su kara kunnuwa da idanu idan sun ga inda ake bukatar tallafi su karfafa guiwar shi.

Hamdala, yace irin wadannan jagororin gwamna Umaru Bago ke bukata da zasu taimaka masa wajen taimakawa al'umma da samar da abubuwan more rayuwa ga talakawa, wanda kudurin gwamna Umaru Bago shi ne kawo sauyi a tsarin siyasar jihar Neja, ta yadda za a cin ma kudurin samar da sabuwar jihar Neja.

Lawal Hamdala, ya jawo hankalin al'ummar yankin Neja ta arewa da su cigaba da hada kai, da yiwa shugabanni addu'o'in alheri ta yadda za a samun zaman lafiya da cigaban yankin.

"Muna bukatar hadin kai, kawar da bambancin jam'iyya ko ubangidan siyasa wanda hakan ne zai baiwa shugabannin mu kwarin guiwar samar mana da romon dimukuradiyya ta hanyar ayyukan raya kasa".

Dattijon ya jawo hankalin wadanda suka samu gajiyar da su yi anfani da abubuwan da suka samu ta yadda zai zama madogarar rayuwarsu har su taimaki wasu.

No comments