Daga Khalid Idris Doya Jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) a jihar Gombe ta kori wani mambanta daga jam'iyyar ...
Jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) a jihar Gombe ta kori wani mambanta daga jam'iyyar tare da cire wasu manyan shugabanninta su uku daga muƙamansu sakamakon zarginsu da yin zagon ƙasa da take-taken da ke janyo ɓaraka da warzaga zaman lafiya da haɗin kan mambobin jam'iyyar.
Shugaban jam'iyyar a matakin jihar, Malam Auwal Abba Barde, shi ne ya sanar da ɗaukan wannan matakin a hirarsa da 'yan jarida, ya ce, an ɗauki matakin ne bayan gudanar da jerin bincike da shawarorin da rassan jam'iyyar suka bayar na yin hakan.
Daga cikin waɗanda lamarin ya shafa akwai Nafiu Bala, wanda jam'iyyar ta kora gaba ɗaya daga cikinta, wadda a baya-bayan nan ya ayyana kansa a matsayin shugaban jam'iyyar na ADC na ƙasa.
Sauran waɗanda aka sallama daga muƙaminsu sun haɗa da mataimakin shugaban jam'iyyar reshen jihar, Nasiru Lawan; sakataren jam'iyyar a jihar, Danladi Ya’u; da kuma shugaban matasa na jam'iyyar reshen jihar, Abdulkadir Sa’idu, wanda aka fi sani da Digiri.
Barde ya yi bayanin cewa shawarar korar Nafiu Bala daga jam'iyyar ya fito ne daga rahoton binciken kwamitin ladabtarwa da ɗa'a na gundumar Nasarawo, wanda ya sameshi da laifin rashin ɗa'a, janyo rarrabuwa da kuma zagon ƙasa wa harkokin jam'iyyar.
Ya ƙara da cewa an gayyaci Bala da kuma wallafawa a jarida domin ya zo a kare kansa kan zarge-zargen da ake masa amma ya kasa zuwa.
"Ayyana kansa a matsayin shugaban jam'iyyar ADC na ƙasa da Nafiu Bala ya yi, ba wai kawai ya ɓata sunan shugabancin jam'iyyar ba ne, har ma ya haifar da ruɗani da rarrabuwar kawuna a tsakaninmu," in ji Barde
Ya ƙara da cewa shugabancin jam'iyyar a matakin jihar ya amince da shawarar da kwamitin binciken ya ɗauka kuma za a aike da matsayar da aka cimma zuwa ga uwar jam'iyyar a matakin ƙasa domin tabbatar da aiwatar da matsayar.
Shugaban ya kuma ce an ɗauki matakan ne domin gargaɗi ga sauran mambobin jam'iyyar da kada su yi rashin ladabi ko ɗa'a zagon ƙasa wa jam'iyyar.
Barde ya kuma tabbatar da cewa jam'iyyar ADC a shirye take wajen shiga babban zaɓen 2027 domin a dama da ita wajen neman kujerun siyasa.
No comments