Daga Zainab Rauf, Abuja Harkar Musulunci a Nijeriya a karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky ta yi kakkausar suka ga sabuwar yarjej...
Daga Zainab Rauf, Abuja
Harkar Musulunci a Nijeriya a karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky ta yi kakkausar suka ga sabuwar yarjejeniyar hadin gwiwar tsaro da tattalin arziki da aka kulla tsakanin gwamnatin Nijeriya da kasar Isra’ila, tana kiran wannan mataki a matsayin cin amana ga al’ummar Falasɗinu da kuma “mummunar kawance” da abin da ta kira da “gwamnatin kisan kare dangi.”
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar
Asabar, 23 ga Agusta, wacce Sidi Munir Sokoto ya sa wa hannu a madadinta, Harkar
Musulunci ta bayyana bacin ranta kan wannan yarjejeniya wacce aka cimma
tsakanin Ministar Harkokin Waje ta Nijeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, da
abokiyar aikinta ta Isra’ila, Sharren Haskel-Harpaz.
Harkar Musuluncin ta zargi Isra’ila da aikata
laifukan yaki a Gaza, tare da sukar gwamnatin Nijeriya saboda shiga huldar
diflomasiyya da tattalin arziki da wata kasa da take fuskantar shari’a a Kotun
Duniya (ICJ) kan laifin kisan kare dangi, wariyar launin fata da laifukan cin
zarafin ɗan adam.
“Wannan ba kawai cin amana ba ne — hadin kai
ne da masu kisa, kuma zunubi ne marar yafuwa ga bil’adama,” in ji sanarwar. “A
daidai lokacin da aka kashe sama da mutane 60,000 a Gaza tun watan Oktoba 2023
— ciki har da mata, yara, tsofaffi da Kiristoci — gwamnatin Nijeriya ta bude
kofa ga wadannan masu zubar da jini ba tare da jin kunya ba.”
Harkar ta tunatar da wasu jawabai da jami’an
gwamnati suka taba yi a baya, suna sukar yadda Isra’ila ke tafiyar da al’amuran
Gaza. A watan Maris 2024, Ministan Harkokin Waje Yusuf Tuggar ya bayyana halin
da ake ciki a Gaza da cewa “ya fi karfin lissafi kuma abin kunya ne.” Haka nan,
Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima a jawabinsa a babban taron Majalisar
Dinkin Duniya karo na 79, ya bayyana goyon baya ga ‘yancin Falasɗinu tare da
yin tir da kisan kare dangi a Gaza.
Harkar Musulunci ta yi tambaya kan dalilin da
ya sa gwamnatin Nijeriya ke canza matsayinta na baya, tana zargin cewa wannan
sabuwar yarjejeniya ta saba wa matsayinta na baya. “Ta yaya wannan gwamnati da
ke sukar laifuka, amma kuma ita ce yanzu ke sa hannu a yarjejeniya da masu
aikata laifukan?” sanarwar ta tambaya. “Wannan ba manufofin wajenmu ba ne —
rushe dabi’unmu ne.”
Sanarwar ta kara da cewa, muradun Isra’ila a Nijeriya
ba na samar da zaman lafiya ko tsaro ba ne, sai dai neman amfani da tattalin
arziki da tsarin leken asiri na kasar don fadada tasirinta a nahiyar Afirka.
Harkar Musulunci ta jaddada kin amincewarta da
duk wata alaka da Isra’ila a Nijeriya, tana kira ga ‘yan Nijeriya masu addinai
daban-daban da su ki amincewa da abin da ta kira “kawance da masu kisa.”
“Gwamnatin Nijeriya ta sayar da mutuncinta. Ta
ci amanar Falasɗinu kuma ta tozarta al’ummar Nijeriya,” in ji sanarwar.
Har
yanzu Ma’aikatar Harkokin Waje ta Nijeriya ba ta fitar da wata sanarwa ba
dangane da korafe-korafen da Harkar Musulunci ta gabatar.
No comments