Iniubong Umoren Daga Muhammad Haruna An tsinci gawar wata matashiyar budurwa mai suna Iniubong Umoren, wanda yake daliba ce da ta karanc...
![]() |
Iniubong Umoren |
Daga Muhammad Haruna
An
tsinci gawar wata matashiyar budurwa mai suna Iniubong Umoren, wanda yake daliba
ce da ta karanci ilimin Falsafa a Jami’ar Uyo dake jihar Akwa Ibom MADOGARA ta labarto.
Majiyarmu
ta FIJ ta labarto cewa; wata makusanciyar matashiyar, Umoh Uduak, ita ce ta
tabbatar da labarin a ranar Lahadi a wani sakon bidiyo da ta wallafa a shafinta
na Twitter, inda take kuka ta bayyana cewa; “sun yi kawata fyade sun kuma kashe
ta”, ta tabbatar.
Kawar
ta ta ta tabbatar da cewa sai da aka yi wa Iniubong fyade sannan aka kashe ta.
Shafukan
sada zumunta ya cika da maganganu iri-iri tun ranar 29 ga watan Afrilun 2021, a
lokacin da Umoh ta aika da wani sakon gaggawa na neman taimako, inda ta yi
zargin an yi garkuwa da kawarta bayan da ta amince ta halarci wani jarabawar
neman aiki a wajen Akwa Ibom.
Umoh
ta rubuta cewa; “ta shaida min cewa za ta je jarabawar neman aiki a airport
road, wanda yake yana da nisa da gidansu. Jim kadan, sai ta aika min da sakon
murya na dakika daya a WhatsApp, sai na kira ta domin na ji ko tana son ta ce
min wani abu ne, amma ina kiranta na fara jin ihu”, ta labarta.
Hakan
ya sanya Umoh ta rubuta a shafinta na Twitter tana neman a taimakawa kawarta
saboda ita a cewarta tana Legas; “kawarku na bukatar taimakon mu. Ni ina Legas
ne ba zan iya taimakonta ba da ya wuce na wallafa sakon nan”, ta tabbatar.
Hakan
ya sanya ‘yan Nijeriya da dama a shafin na Twitter suka kaddamar da kamfen da
HashTag na #FindHinyUmoren, domin binciko wannan matashiryar budurwar, inda
daga bisani ‘yan sanda suka cafke mutum biyu da ake zargi a bacewarta.
Kwanaki
biyu kafin bacewar Iniubong ta wallafa tana neman aiki a shafinta na Twitter,
inda ta rubuta cewa; “ku taimaka ina matukar bukatar aiki, wani abu da zan rika
yi da zai taimakawa jikina da ruhina a yayin da nake bada gudummawata ga
kamfanin”, ta rubuta.
Ta ci
gaba da cewa; “ina zaune ne a Uyo, ina da fasaha, ina da kwazon wajen zurfin
tunani, abu mafi muhimmanci ina da saurin fahimtar abu. Idan an bukaci na tura
CV dina zan yi hakan”, ta wallafa cikin harshen Turanci a ranar 27 ga watan
Afrilun 2021.
No comments