Rahotanni sun nuna cewa; a ranar Asabar bangarorin da ke cikin yarjejeniyar nukiliyar Iran sun tashi daga zagaye na uku na taron da suke a...
Rahotanni
sun nuna cewa; a ranar Asabar bangarorin da ke cikin yarjejeniyar nukiliyar
Iran sun tashi daga zagaye na uku na taron da suke a wani mataki na maido da
Amurka cikin yarjejeniyar, inda ita ma Rasha ta bayyana kwarin gwiwar cewar
za a cimma gaci nan da makonni uku masu
zuwa.
Wata
majiyarmu ta diflomasiyya daga manyan kasashen da ke cikin yarjejeniyar ta
shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa ba a kai ga fahimtar juna ba
game da muhimman batutuwa ba, amma babu abin da zai gagara.
Jagoran
tawagar Iran a taron, kuma mataimakin ministan harkokin wajen kasar, Abbas
Araghchi ya ce tattaunawar ta kai wani muhimmin mataki.
Yarjejeniyar
nukiliyar Iran na cikin halin rai kwakwai-mutu-kwakwai tun bayan da tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya janye kasarsa
daga cikinta a shekarar 2018.
No comments