A yau Lahadi Koriya ta Arewa ta zargi shugaban Amurka Joe Biden da bin manufofin nuna kiyayya, tana mai watsi da abin da ta kira diflomasi...
A yau Lahadi Koriya ta Arewa ta
zargi shugaban Amurka Joe Biden da bin manufofin nuna kiyayya, tana mai watsi
da abin da ta kira diflomasiyyar yaudara ta Amurka, inda ta yi gargadin mayar
da martani a kan duk wani cin zali da za a yi mata.
A ranar Laraba da ta gabata Biden ya
ce gwamnatinsa za ta magance barazanar shirin nukiliyar Koriya ta Arewa ta
hanyar diflomasiyya da takatsantsan kamar yadda RFI ta labarto.
A ranar Juma’a fadar White House ta
ce a shirye shugaba Biden yake don tattaunawa da Koriya ta Arewa a kan batun
jingine shirin nukiliyarta, biyo bayan kammala nazarin manufofi, amma Pyongyang
ta mayar da martani tana cewa, Biden ya tafka babban kuskure.
No comments