Nijeriya za ta karbi karin taimakon allurar rigakafin cutar korona kyauta a karkashin shirin Covax da yawan sa ya kai miliyan 4 nan da wat...
Nijeriya
za ta karbi karin taimakon allurar rigakafin cutar korona kyauta a karkashin
shirin Covax da yawan sa ya kai miliyan 4 nan da watan Agusta mai zuwa.
Shi
dai wannan shirin tallafin Covax an shirya shi ne domin taimakawa kasashe
matalauta wajen ganin sun samu damar yiwa al’ummar kasashen su miliyan 80 daga
cikin kasashe da yankuna 129 na duniya rigakafin cutar.
Nijeriya
mai dauke da mutane sama da miliyan 200 ta karbi kashi na farko na maganin
rigakafin cutar samfurin AstraZeneca a watan Maris wanda tuni aka yiwa wasu
daga cikin jama’ar ta allurar kamar yadda Rfi Hausa ta labarto.
Shugaban
Hukumar kula da lafiya a matakin farko Dr Faisal Shuaibu ya kuma bayyana cewar
gwamnatin kasar za ta sayi maganin rigakafin kirar Johnson & Johnson kusan
miliyan 30 ta hannun kungiyar kasashen Afirka ta AU da AfreximBank nan da watan
Satumba mai zuwa, bayan kammala amfani da allura kusan miliyan 4 a matakin
farko.
Shuaibu
ya bukaci masu jan kafa wajen karbar allurar da su kauda duk wani shakku da
suke da ita wajen gabatar da kan su domin yi musu rigakafin wanda yace bashi da
wata illa.
Cutar
korona ta hallaka mutane 2,119 daga cikin 167,467 da aka tabbatar sun harbu da
ita a Najeriya.
No comments