Gwamnatin Tarayya ta tsawaita dokar hana baki daga kasashen Brazil da India da Turkiya shiga cikin kasar ta saboda dakile yaduwar cutar ko...
Gwamnatin
Tarayya ta tsawaita dokar hana baki daga kasashen Brazil da India da Turkiya
shiga cikin kasar ta saboda dakile yaduwar cutar korona wadda tayi kamari a
cikin kasashen su.
Gwamnatin
kasar ta kuma sanya sunan Afirka ta Kudu cikin jerin kasashen dake nahiyar
Afirka da dokar ta shafa bayan kasashen Zambia da Rwanda da Namibia da kuma
Uganda.
Shugaban
kwamitin yaki da cutar kuma Sakataren Gwamnati Boss Gida Mustapha ya sanar da
sabon matakin inda ya kara da cewar sabuwar dokar za tayi aiki na makwanni 4
kafin sake nazari akan ta.
Mustapha
yace suna sanya ido akan abubuwan dake faruwa a kasashen duniya dangane da
abinda ya shafi cutar domin daukar matakan da suka dace na kare lafiyar Yan
Najeriya.
Sakataren
Gwamnatin ya baiwa Yan Najeriya shawarar ci gaba da sanya ido sosai da daukar
matakan kare lafiyar su ganin yadda ake samun sake dawowar cutar a wasu
kasashen Afirka.
Shugaban
kwamitin ya kuma bayyana cewar suna mayar da hankali akan batun samar da
maganin rigakafi wajen ganin an yiwa jama’ar kasar allurar domin kare kan su
daga harbuwa da cutar.
No comments