Daga Ammar Muhammad Gwamnatin Tarayya ta bukaci gwamnonin jihohin arewacin kasar, Sarakuna da sauran masu ruwa da tsaki da su dakatar ...
Daga
Ammar Muhammad
Gwamnatin
Tarayya ta bukaci gwamnonin jihohin arewacin kasar, Sarakuna da sauran masu
ruwa da tsaki da su dakatar da bukukuwan hawan Sallah babba domin dakile
yaduwar annobar Korona da gwamnatin Tarayyar ta ce tana kokarin dawowa da
karfinta.
Sakataren
Gwamnatin Tarayya kuma Shugaban Kwamitin yaki da annobar Korona na Nijeriya,
Boss Mustapha ne ya fitar da sanarwar a ranar Lahadi a birnin Tarayya Abuja.
Matakin
gwamnatin Nijeriyar dai ya biyo bayan sanya jihohi shida da kuma birnin Abuja
cikin matakin tsaurara matakan dakile yaduwar Korona, annobar da wasu kwararru
kan sha’anin lafiya ke gargadin yiwuwar sake barkewarta a zango na uku, idan ba
a dauki matakan da suka dace ba.
Jihohin
da lamarin ya shafa dai sun hada da Legas, Oyo, Kano, Filato, Kaduna, Ribas da
kuma birnin Tarayya Abuja.
Masarautar
Zazzau dai dake jihar Kaduna na daya daga cikin masarautun dake shirin gudanar
da Hawan Sallah a bana, amma ganin wannan sanarwa ta kwamitin dakile yaduwar
cutar korona ta gwamnatin Tarayya, wadansu na hasashen cewa hakan na iya tilasta
a soke hawan sallar da aka shirya gudanarwa
ganin yadda gwamnan jihar, Malam Nasiru El-Rufai na daya daga cikin gwamnonin dake yaki da cutar korona tun bayan bullarta a Nijeriya a cikin watan Fabarairun
2020.
![]() |
Hawan Sallah a masarautar Zazzau |
No comments