Daga Awwal Umar Kontagora A cigaba da yunkurin tabbatar gudanar da ayyuka bisa doka a yankunan kananan hukumomi, kungiyar Nigeria Union of...
Daga Awwal Umar Kontagora
A cigaba da yunkurin tabbatar gudanar da ayyuka bisa doka a yankunan kananan hukumomi, kungiyar Nigeria Union of Mine Workers ta gabatar da shaidar rantsuwa da dokokin kungiyar ga shugabannin kungiyar na karamar hukumar Shiroro.
Mika takardar ga shugabannin bayan rantsuwa da suka sha biyu ga watan Fabrairun wannan shekarar, ya ba su damar fara ayyukan kungida gadan gadan.
Da yake tsokaci a wajen taron, shugaban kungiyar a jihar Neja, Comr. Musa Nasko yace rantsar zababbun shugabannin a matakin kananan hukumomi da su ragamar cigaba da aiki, zai taimakwa kungiyar wajen samun sauki da tantance halastattun masu aikin hakar ma'adani. Yace idan kananan hukumomi suna aiki sun sauwaka shugabannin kungiyar na jiha, su kuma sai su samar fuskantar abubuwan da ke tasowa a jiha.
Karamar hukumar Shiroro, tayi muna adalci kuma ta nuna goyon bayanta gare mu domin yau a cikin council muke gabatar da wannan aikin. Idan ka lura tsakanin shugabannin kungiyar na karamar hukumar Shiroro da ita kan karamar hukumar akwai kyakkyawar fahimta a tsakaninsu.
Ita karamar hukumar da ke korafin bata samun komai daga harkar hakar ma'adani idan suka hada kai da shugabannin NUMW na karamar hukumar za a bullo da tsarin da ita ma za ta rika samun kudaden shiga.
Saboda haka, ina jawo hankalin wadannan shugabannin da zasu fara aiki yau, da su ji tsoron Allah su yi aiki bisa adalci, domin adalcin nan ne zai janyo masu gamsuwa da amincewa daga yayan kungiyar ta karamar hukuma.
Shi kuwa, shugaban NLC reshen karamar hukumar, Comr. Ishaya Hassan Galadima cewa yayi maganar gwagwarmaya, magana ta kwatar yanci da kare hakkin al'umma, saboda haka ya jawo hankalin shugabannin da su zo su hada kai da NLC duk wasu matsalolin da zasu taso ba sai sun tunkari uwar kungiya ta jiha.
A yanzu sun zama yayan kunguyar kwadago a karamar hukumar nan, za mu aiki kafada da kafada domin ganin karamar hukumar mu, da jihar Neja da kasar mu sun anfana da shirin hakar ma'adani a karamar hukumar Shiroro.
Hon. Sanusi Sa'idu sakataren karamar hukumar Shiroro kuma wakilin shugaban karamar hukumar, Hon. Akilu Kuta, ya jawo hankalin shugabannin ne da su baiwa karamar hukumar hadin kai samun kudaden shiga, hada kai wajen kawar da baragurbi ganin halin rashin tsaro da karamar hukumar ke fuskanta.
Hon. Akilu, ya cigaba da cewar karamar hukumar Shiroro na daya kuma sahun gaba a cikin kananan hukumomi da aikin ma'adani ke da tasiri, amma duk da wannan damar karamar hukumar ba ta anfana da komai, saboda haka akwai bukatar ganin an samar da hanyoyin samun kudaden shiga ga karamar hukuma.
Comr. Abdul'aziz Mohammed She, shi ne shugaban kungiyar a karamar hukumar, yace muna biyan hakkokan gwamnati daga kamfanoni masu zaman kan su da kungiyoyin kofarabtif da ke karkashin NUMW, ba wani tallafin kayan aiki da muke samu daga bangaren gwamnati.
Da karamar hukumar Shiroro za ta samar mana kayan aiki na zamani koda haya ko ta sayar mana cikin saukin farashi, ina da tabbacin kudaden shigar da karamar hukuma za ta rika samu a bangaren mu ba wata karamar hukuma da za ta iya samar da shi.
A karamar hukumar Shiroro ba mu da kalubalen da ya wuce rashin kayan aiki, domin yanzu baki ke shigowa da kayayyakin suna ba mu da tsada wanda tilas yasa wasu lokuttan aikin ke tsayawa a karamar hukumar Shiroro.
Abdul'aziz, ya kara da cewar ina jawo hankalin mambobin mu muhimmancin yin rajista da kungiya dan tantance mutum kafi ba shi katin shaidar zama dan kungiya, ba wani da za yiwa gata muddin ba kai rajista da NUMW ba duk abinda ya taso ba za mu saurare ka ba.
" Ina mai jawo hankalin yan uwana da aka dora mana wannan nauyin da su ba ni hadin kai dan yin aiki tare, duk wata matsala idan ta taso a fuskance kai tsaya, domin za mu tabbatar mun yi tafiya da kowa bisa doka, kuma za mu tabbatar da kare martabar sana'ar nan domin cigaban kan mu, karamar hukuma da jihar mu baki daya.
No comments