Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Uwar Kungiyar NUMW Ta Damka Dokokin Kungiya Da Tsare Tsaren Kamun Aiki Ga Reshen Kungiyar A Neja

Daga Awwal Umar Kontagora Kungiyar leburori masu hakar ma'adanan kasa a jihar Neja ( Nigeria Union of Mine Worker) ta damka dokokin kung...


Daga Awwal Umar Kontagora

Kungiyar leburori masu hakar ma'adanan kasa a jihar Neja ( Nigeria Union of Mine Worker) ta damka dokokin kungiya da tsare tsaren kamun aiki ga rantsantesn shugaban kungiyar, Comr. Usman Bashar.

Tunda farko a bayaninsa ga manema labatai, shugaban kungiyar ta jihar Neja, Comr. Musa Adamu Nasko ya bayyana cewar tun bayan rantsar da reshen kungiyar a karamar hukumar Magama, ba su fara aiki ba dan ba a ba su time and shedule ba.

Amma bayan mun kammala tsare tsare kamar yadda dokokin kungiya ta tanada yau asabar mun kammala komai kuma mun damka masu aikin. Saboda haka yanzu wajibi ne su bi dokokin kungiya sau da kafa kuma su tabbatar sun tsaya wajen kare martabar kungiya da dokokin kasa.

Nasko ya janyo hankalin shugabannin da su hada kai da gwamnati da jami'an tsaro wajen tsaftace aikin hakar ma'adani a yankin karamar hukumar su.

Gwamnatin jiha, ta sahale mana yin aikin mu ba tare da kutse ba, kuma tsare tsaren da gwamnatin ta gabatar mana mun fahimci bai sabawa dokokin kasar nan ba, mun rungume shi hannu biyu, wajibi ne kowani mamba, ya tabbatar da yana biyan kudaden shigar gwamnati da na kungiya kuma su hada kai da jami'an tsaro wajen ganin an dauki mataki akan dukkan wani abinda zai kawo masu tsaiko a lokacin gudanat da aikinsu.

A bayaninsa, Comr. Usman Bashir Magama, ya yabawa uwar kungiyar ta jiha bisa goyon bayan da take baiwa yayan kungiyar musamman wajen tsaya masu akan dukkanin wasu matsaloli da ke tasowa.

Yau mun amshi tsare tsaren tafiyar da kungiya a hukumance, kuma za mu tabbatar mun bi su kamar yadda suke. Sai dai ina jawo hankalin yan uwana zababbu kamar yadda suka uwar kungiya ta jiha na gudanar da ayyukanta, ina kira a gare su da su ba ni goyon baya wajen ganin karamar hukumar Magama ta zama ta farko a wajen gudanar da aiki mai tsafta kamar yadda dokokin kungiya ta tsara.

Ina kuma jawo hankalin abokan aikin mu da suka fito daga wasu kungiyoyi da su sani NUMW ba abokiyar hamayyarsu ba ne, da su zo mu hada kai dan tafiyar da aiki ba tare da mun yiwa juna kutse ba.

Comr. Usman ya janyo hankalin yayan kungiyar na karamar hukumar Magama da su ba su hadin kai, suma a shirye suke wajen kare mutuncinsu da tsayawa akan duk wata matsalar da ta tunkaro su.

Alhaji Yahaya Anfani, shi ne mai bincike na uwar kungiyar kuma dan asalin karamar hukumar Magama, ya jawo hankalin kananan hukumomin Bargu, Agwara, da Mashegu da su gaggauta kammala shirye shiryen dan rantsar da su kamar yadda karamar hukumar Magama tayi.

Yace, muna kokari ne a kungiyance wajen tabbatar da mun tsare tsaren da gwamnatin jiha ta samar wajen tsaftace harkar hakar ma'adanan kasa a jihar nan. Don haka duk wani yunkurin karya doka ba za mu sanya idanu ba ganin gwamnati ta ba mu wuka da nama wajen ganin ana bin dokoki kamar yadda aka tsara.

Haka kuma, ya yabawa jami'an tsaro wajen ba su hadin kai da amincewar yin aiki tare dan tsaftace aikin hakar ma'adani a jihar Neja.

Taron mika takardun an gudanar da shi ne a sakatariyar uwar kungiyar da ke minna ranar asabar din makon nan bisa jagorancin shugaban kungiyar ta jiha, Comr. Musa Adamu Nasko.

No comments