Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

MOGGAL FULBE Ta Bude Sakatariyar Kungiyar Reshen Jihar Neja

Daga Awwal Umar Kontagora Sabuwar kungiyar MOGGAL FULBE PULAKO Development Association of Nigeria bisa jagorancin Alhaji Abdullahi Bodo na j...


Daga Awwal Umar Kontagora

Sabuwar kungiyar MOGGAL FULBE PULAKO Development Association of Nigeria bisa jagorancin Alhaji Abdullahi Bodo na jihar Neja ta bude sakatariyar kungiyar reshen jihar Neja.

Tunda farko a bayaninsa, tsohon kwamishinan ma'aikatar jin dadi da walwalar makiyaya da manoma ta jihar Neja, Hon. Ahmed Sanda Rebe ya yabawa gwamna Umar Mohammad Bago na cika alkawalin baiwa Fulani makiyaya damar taka rawa a gwamnatinsa. Cikin shekaru biyu da kafa wannan maaikatar mun samu nasarori da dama, domin mun samun cigaba kashi saba'in na matsalolin makiyaya sun kau a wannan gwamnatin.

Daga cikin matsalolin da muke fuskanta na rashin jituwa tsakanin manoma da makiyaya mun dauki mataki akan shi a gwamnatance, matsalolin rashin ilimi ga yayan makiyaya gwamnatin Umar Bago ta dauki mataki akan shi.

Tsohon kwamishinan ya cigaba da cewar al'ummar Fulani su na goyon bayan gwamnatin nan sau da kafa sakamakon ba su damar ba su damar taka rawa da gwamnatin tayi ba tare da sun jingina da kowa ba ta hanyar kirkirar wannan ma'aikatar.

Ahmed Rabe, ya jawo hankalin Fulani da su cigaba da hada kai kar su bari yawaitar kungiyoyi ya zamo sanadin samun rarrabuwan kawuna a tsakaninsu. Kan haka ya yabawa shugaban kungiyar MOGGAL ta kasa, Alhaji Sani Juli bisa aza harsashen wannan tafiyar a jihar Neja.

A bayaninsa, shugaban kungiyar ta kasa, Alhaji Sani Juli, yace duba da irin kungiyoyi da ake kafawa a kasar nan, yawan al'ummar Fulani a kasar nan, ko kungiya nawa aka kafa ba zai zama barazana ga cigaban kasa ba, domin matsalolin na da yawa kuma kowace kungiya da bangaren da zata fi mayar da hankali dan anfanar al'ummar Fulani.

Yau mun tsinci kan mu a wani yanayi na rashin tsaro wanda mu al'ummar Fulani da abokan zaman mu kowa na ji a jikin shi, amma ganin yadda gwamnatin Neja ya zabura wajen fuskantar matsalolin Fulani makiyaya musamman maganar ilimi dole mu tashi tsaye wajen taimaka ma ta, domin samun nasarar gwamnatin nan, nasarar mu baki daya.

Saboda haka, maganar rikice rikicen Fulani da Manoma hanyar da gwamnatin ta bullo da shi abin a yaba ne, babu wani dalilin da wani zai yi korafi a yanzu, domin sarakunan gargajiya da jami'an tsaro suna ba mu goyon baya wajen samun sulhu ba tare da kai ruwa rana ba.

Za mu jinjinawa tsohon kwamishina Hon. Ahmed Sanda wajen ganin yawaitar garkame Fulani da jami'an tsaro kan yi a baya sakamakon rashin fahimta da za a iya walwale shi a karkashin bishiya da kan dauki lokaci, wanda kan haifar da cin zarafi a wasu lokuttan ya kawo karshe.

Ai bafillatani makiyayi da manomi yan uwan juna ne, kuma ko tsakanin harshe da hakori sukan samu sabani amma hakuri da juna shi ke kawo zaman lafiya.

Hajiya Aisha Mohammad, itace shugabar mata na kungiyar a jihar Neja. Ta yabawa gwamnatin jiha bisa bullo da shiraruwa dan anfani matan Fulani.

A cewarta gwamnatin Umar Bago, ta bullo da samar da runfuna da kawar da yawon tallace tallacen matan Fulani, wanda a yau idan mutum zai sayi fura da nono ya san inda zai tafi dan gwamnatin ta samar da matsugunni ga masu sana'ar. Sai tace kamar yadda gwamnatin ta samar da irin wannan matsugunnin a Minna ya kamata sauran kananan hukumomi ashirin da hudu a samar da su.

Sannan ta janyo hankalin mazaje da su umurci matan su da yayaansu wajen mallakar katin zabe da hukumar zabe ta kasa ke kan aikinsa a yanzu. Kuma ta yi kira da cewar tsarin na bukatar kulawa sosai domin a yanzu ofisoshin hukumar zabe na kananan hukumomi da sakatariyar hukumar ta jiha kawai ake iya yin rajistan, akwai bukatar a fadada aikin zuwa runfunar zabe ta yadda duk wanda ya kai shekarun mallakar katin zaben bai da shi ko yayi hijira daga inda ya fito zai samu damar mallakar katin.

Alhaji Shehu Danfulani sarkin fulanin Limawa, kuma mataimakin shugabannin kungiyar a jihar Neja, ya yabawa Fulani makiyaya wajen hada kai da amincewa dan samun zaman lafiya, a cewarsa muddin mu ka cigaba da yadda ake tafiya yanzu muna da kwarin guiwar zaman lafiya zai dawo a kasar nan, domin gwamnati da jami'an tsaro su na abinda ya dace.

Jagoran Fulani kuma tsohon shugaban Miyetti Allah Cattle Breaders ta kasa, Alhaji Hussaini Yusuf ( Jarman Chinbi) da ya samu wakilcin Ardon Bosso, Alhaji Isma'ila Rebe, ya jawo hankalin Fulani da su cigaba da baiwa gwamnati hadin kai da goyon baya, a cewarsa gwamnatin jihar Neja bisa jagorancin babban manomin jiha, Dr. Umar Mohammad Bago, da gwamnatin tarayya bisa jagorancin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu suna kokarin kawo sauye sauyen da zasu kawo cigaba a kasar nan.

Saboda haka, ko kirkirar ma'aikatar jin dadin manoma da makiyaya da gwamnatin Neja ta yi da kuma samar da ma'aikatar kula da harkokin kiwon dabbobi da gwamnatin tarayya ta yi abin a yaba ne kuma a cigaba da ba su goyon baya.

Taron dai ya samu halartar Fulani daga sassan kasar nan da suka hada da jahohin Adamawa, Legas, Benue da makotan kasar nan.

No comments