Daga Muhammad A. Dalhatu Rahotannin dake shigo mana na nuni da cewa; masarautar Kano ta soke bukukuwan hawan Babban Salla. Kafar watsa l...
Daga Muhammad A. Dalhatu
Rahotannin
dake shigo mana na nuni da cewa; masarautar Kano ta soke bukukuwan hawan Babban
Salla.
Kafar
watsa labarai ta Solacebase ta labarto
cewa; masarautar ta soke bukukuwan sallar ne sakamakon shawarwarin da gwamnatin
Tarayya ta bayar saboda dawowar annobar cutar korona a karo na uku.
Madakin
Kano, Alhaji Yusuf Nabahani ya tabbatar
da ‘yan jarida hakan a yau Litinin.
Alhaji
Yusuf Nabahani ya ce Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya ba shi umurnin ya
sanar da dukkanin Hakiman dake karkashin masarautar wannan umurnin.
Dama
MADOGARA ta labarto cewa; kwamitin dake
yaki da annobar cutar korona ta gwamnatin Tarayya a karkashin ofishin Sakataren gwamnatin Tarayya ta shawarci jihohi shida ciki harda
birnin Tarayya Abuja da su soke bukukuwan Sallah domin cutar korona ‘yar Delta
ta dawo gadan-gadan a kasar.
Jihohin
sun hada da Legos, Oyo, Ribas, Kaduna, Kano, da Filato.
No comments