Rfi Hausa ta labarto cewa; shugaban Amurka Joe Biden ya gargadi Amurkawa cewar har yanzu annobar korona na nan tana barazana ga jama’a, ya...
Rfi Hausa ta labarto cewa; shugaban Amurka Joe Biden ya gargadi
Amurkawa cewar har yanzu annobar korona na nan tana barazana ga jama’a, yayin
da jama’ar kasar suka fara komawa rayuwar su ta yau da kullum.
Yayin da yake jawabin ranar yancin a gaban baki akalla 1,000 a
fadar White House ya jinjinawa mutanen kasar sama da 600,000 da suka rasa
rayukan su sakamakona annobar, yayin da gwamnatin sa ke kokarin hada kan
jama’ar kasar sakamakon rarrabuwar kawunan da aka samu a lokacin tsohon
shugaban kasa Donald Trump.
Biden ya bayyana shekarar da ta gabata a matsayin mafi muni a
tarihin kasar, yayin da kasar ta fara ganin haske.
Biden ya ce Amurka na dab da ayyana samun yanci daga annobar
korona, sakamakon tasirin allurar rigakafin da aka samar, inda tuni tattalin
arzikin kasar ya kama hanyar mikewa.
No comments