*Samar Da Dunkulalliyar Kasa Shi Ne Buri Na, Inji Sarki Bayero *Tsiraru Ke Kiran Raba kasa Don Muradin kashin Kansu, Sarkin Kan...
*Samar Da Dunkulalliyar
Kasa Shi Ne Buri Na, Inji Sarki Bayero
*Tsiraru Ke Kiran Raba
kasa Don Muradin kashin Kansu, Sarkin Kano
*Banbancin Da Ke
Tsakaninmu Bai Kai Abubuwan Da Suka Hada Mu Ba
Gagarumin bikin mika
Sandar Mulki ga Sarkin Kano, ALHAJI AMINU ADO BAYERO, zai wakana a yau a
katafaren farfajiyar filin wasanni ta Sani Abacha, kuma a daidai wannan wajen
ne marigayin mahaifinsa, Alhaji Ado Bayero ya samu sarautar Sarkin Kano shekaru
53 da suka gabata.
A wannan hirar ta
musamman da jaridar LEADERSHIP Weekend ta yi da shi cikin harshen turanci wanda
KHALID IDRIS DOYA ya fassara, mai martaba sarkin yi magana kan batutuwan da
suka shafi kasa, ciki har da batun kiraye-kirayen raba kasa ko masu neman
ballewa, wanda ya ce an samar da wadannan batutuwan ne kawai bisa son zuciya da
son kai na wasu kalilan don manufarsu ta daban. Ya kuma yi magana kan sauyin da
ya samu a rayuwarsa daga dan Sarki zuwa hadewa kan karagar mulkin Sarki da ya
nuna hakan a matsayin abun da ya zo masa da sauki matuka. Ga hirar:
Mai
Martaba, ya ka tsinci kanka daga sauyi Yarima zuwa Sarki?
Ka ce sauyi ba zan ce
na yarda ko ban yarda ba. Maganar gaskiya ita ce ni an haifeni a cikin wannan
tsarin na sarauta; na kuma taso cikin tsari; kama-kama na girma dukka a cikin
tsarin. Don haka ba wani abu ne sabo a garen ba.
Abun da ya zama sabo
kawai shi ne zama a kujerar Kakannina. Ba lamari ne mai sauki ba, musamman idan
aka yi la’akari da halin da ake ciki a yanzu, a matsayinka na shugaba kuma
jagora idan lamari ya kasance mawuyaci ga jama’anka kai ne mai daukan nauyin
wannan batun.
Kai ne za ka dauki nauyin a kanka. A zahirance zan iya cewa wannan shi ne babban kalubalen da nake fuskanta.
Watakila a lokacin da
nake matsayin saurayin mutum ko na ce a lokacin da nake rike da sauratar da ke
da wani iyaka a cikin al’umma, to amma yanzu komai ya faru za ka ji shi, don
haka sauyin ya zo min cikin sauki da saukka saboda na kasance a cikin tsarin
tun usuli wanda na taso a hakan kuma na koyi abubuwa da daman gaske tun kafin
yau.
Tun 1990 na kasance
cikin lamarin ita kanta. Don haka gabaki daya sai mu ce mun gode wa Allah tare
da addu’ar ya cigaba da taimakonmu da agaza mana.
Kasancewarka wanda ka
taso a cikin tsarin sarauta, shin ka taba tsammanin za ka zama Sarki wata rana?
Duk wanda dai ya fito
daga cikin gidan Sarauta fatansa shi ne wata rana ya zama ya gaji iyayensa da
Kakakinsa ya zama shi ne shugaba na mai jan gaba.
Amma ba lamari ne
a-yi-ko-a-mutu ba. Abu ne da aka rigaya aka kaddara.
Babban Yayanku zai iya
zama Sarki; karamin dan uwanka zai iya zama Sarki; hatta ma danka zai iya zama
Sarki. Don haka, fata ne kuma addu’a ne ga duk dan gidan sarauta na wata rana
zai iya zama Sarki idan har Allah ya amince masa kuma ya kaddara masa hakan
cikin rayuwarsa to la-shakka sai ya zama Sarkin nan wani lokaci.
Gaba daya dai, ba zan
ce na yi mamaki ba amma abu guda da zan ce shi ne Allah ne ya maidani abun da
na zama a yau. Na zama Sarki ba wai don na fi kowa ba ne, ba wai don na fi kowa
arziki da dukiya bane.
Allah ne ya kaddara ya
kuma maidani zuwa Sarki. Ina cike da godiya ga ni’imar Allah kan wannan kuma
fatana da rokona zai cigaba da agaza mana da taimakona wajen tafiyar da wannan
nauyin da ke kaina.
Gwamnan Jihar Kano, a
yayin gabatar maka wasikar nadinka kai da saura a matsayin sabbin Sarakuna a
shekarar da ta gabata, ya ce kai da dan uwan Sarkin Bichi, kun zama a tarihi ku
ne na farko a Nijeriya ko Afrika da aka fara nadawa a matsayin Sarakuna masu
daraja ta daya a lokaci guda kuma a jiha. Ya ce, wannan ya faru ne sakamakon
nagartaccen aikin da marigayin mahaifinku wanda ya zama sarki na tsawon shekara
53 ya gudanar, Marigayi Alhaji Ado Bayero, hakan kuma bai rasa nasaba da la’ari
da kyakkyawar jagoranci da tarihi na kwarai da ya kafa ba.
Ta
yaya kake yunkurin daurawa daga irin salon da mahaifinka ya tsaya na kafa
tarihin kwarai?
Gaba daya dai, lokacin
da kake magana kan jagoranci da yadda nake kallo, duk ya shafi meye gadon da ka
gada ni kuma ina kan aiki ne kan ababen da na gada daga wajen marigayi Sarki
tun 1990 har zuwa 2014 lokacin da ya rigamu gidan gaskiya (Allah Jikansa).
Ina godiya wa Allah
domin na samu damar rayuwa mai tsawo da shi wanda na koyi abubuwa daban-daban
da suke taimakona da da kuma yanzu. kokarin kwatanta kanmu da marigayi Sarki abu
ne mai wuya, amma kallon tsarinsu da salonsu wajen tafiyarwa da harkokin mulki
zai taimaka mana sosai wajen kyautata shugabanci na kwarai.
Don haka, ina ganin
babban kalubale a gabana amma niyya ta kwarai zai taimaka tare da goyon bayan
jama’a, musamman ‘yan majalisata, sauran hakimai, masu rike da sarautu,
gwamnati, ‘yan kasuwa, malamai da jama’a, ina tunanin da goyon bayan za mu samu
nasarar kafa tarihin kwarai da jama’a za su jima suna tunawa da mu.
Masautar Kano tana da
dadadden tarihi, tsohowar masarauta mai girman mulki kuma duk da sauyin zamani
har yanzu tana nan da karfin ikonta daram.
Mene
ne sirrin?
Sirrin shine gaskata
abun da muka yi amannar shine daidai. Al’ada da al’adu, kamar yadda kuka ce,
bangare ne na rayuwa muddin kuka rasa al’adarku da al’adunku, babu inda za ku
dosa a rayuwa.
A kowani lokaci na kan
kasance cikin farin ciki da annashuwa idan na ga matasanmu sun rungumi
al’adarsu sosai, don ana cewa, ‘Komai ka gani a rayuwar matasa sannu a hankali
ba zai taba bacewa ba’.
Na yi amannar mutane
sun rungumi al’ada tun da farko, mutane sun yi amanna da al’adu; sun kuma gamsu
da al’adu suna kuma mutuntawa.
Wannan hanyar, aikin
rike al’adu na nan ana kai. Abu kawai da kuke da bukata shine a samu wani da
zai jagoranci gina al’ada da al’adun jama’arsa, tare da gadon iyaye da kakanni
kan abubuwan da suka tafi suka bari.
Wannan shine nake ganin
iyaye da kakanni sun yi tsawon shekarun da suka kasance masu sadaukarwa wajen
rike al’adu da wanzar da su tare da ganin an tabbatar da bunkasa al’adu. Wannan
ya taimaka mana sosai ya kuma taimaka wa jama’anmu da mabiyanmu sun kuma gamsu
da hakan, muma za mu kara azama da himma a wannan fanni domin daukaka darajar
masarautar Kano da al’ummarmu.
Mai
Martaba, daga lokacin da ka hau kujerar Kakaninka zuwa yau, masarautar Kano, ta
bunkasa, fadar jihar ta samu nasarori wajen gudanar da nargartattun ayyuka. Wasu
abubuwa ne kuka kawo domin bunkasa masarautar Kano?
To, idan kuna magana
kan jagorancin masarauta, muna magana ne a kan daurawa bisa tafarkin iyaye da
kakanni da kuma yin ayyukan da za su bunkasa ababen da suka bar mana.
Ina tsammanin a bayyana
wannan shine asalin dalilin nasarata. Kamar yadda nake cewa ina cikin tsarin
sarauta sama da shekaru 30 da suka wuce kuma wadanda ban hadu da su ba lokacin
da suke mulki na karanci tarihinsu kuma na koyi yadda suka tafiyar da
masarautar da yadda suka sanya komai a muhallinsa da ya kai ga basu nasarorin
da suka cimma inganta jihar da ma kasa baki daya. Don haka, ina mai cikin farin
ciki da aka nadani ina mai karamin shekaru.
Aiki tare da marigayi
sarki na tsawon shekara 24 ko makamancin hakan ya taimaka min sosai wajen
tafiyar da ragamar mulki da kuma gabatar da ababen da na koya daga wajen
marigayi Sarki, Abdullahi Bayero, marigayi Sarki Sanusi, tsohon sarkin da na yi
aiki a karkashinsa, dukkaninsu sun taimaka min wajen yin ayyukan da nake yi a
yau, kuma abu mai gayar muhimmanci shine yadda Allah ya azurtani da hazikan
mambobin majalisar Sarki.
Mun kasance masu hada
kai waje guda domin fito da ababen da za su taimaka wa al’ummarmu. Suna ba ni
muhimman kuma nagartattun shawarorin da suka dace ina neman karin hakan domin
cigaba da gudanar da ayyuka na kwarai don al’ummar mu.
Akwai kiranye-kiranyen
da aka yi ta yi na raba kasa ko ballewar wasu sassan kasa. A matsayinka na
Basarake wanda ke da dumbin sani kan tarihin kasa kana da kake kula da al’adun
mutane mabanbanta, menene kake tunanin ya janyo irin wannan batun ballewar wasu
gungu daga kasar kuma me hakan zai iya janyo wa kasar?
Kamar yadda na fada ma
abokan aikinku da farko, idan ka zauna da wani da ya fito daga yankin Kudu ko
Arewa kuka yi magana kan dukkanin batutuwan sake fasalta kasa, abun da zai fada
maka zai sha banban da abun da wani mutum din ma zai fada maka da suka fito
daga yanki guda.
Kamar ma dai akwai
rashin fahimta a tsakanin wadanda suke ganin sun yi zurfi kan wannan bukatar,
kawai abun da ke akwai ra’ayoyi ne na wasu mutane kalilan da suke son kare muradinsu
da son ransu, batu ne na muradin kashin kai.
Don haka, bari mu kalli
wadanda suka yi sadaukar suka yi hidima da ake kiransu masu ruwa da tsakin da
suka zage damtsensu har Nijeriya ta kawo inda take a yau. Su zo su hada kansu
su duba, ‘yan banbance-banbancen da suke akwai kalilan ne idan aka kwatanta da
abubuwan da na yi imanin sun hada a tarayya.
Sannan, na yi amannar
dukkaninmu, masu ruwa da tsaki, ciki har da gwamnonin jihohi, Sarakuna, da
sauran sassan al’umma, za mu iya hada kanmu waje guda da tsarkakekken zuciya,
tabbas da za mu iya fito da mafita kan dukkanin ‘yan matsalolin da suke akwai.
Kamar yadda na ce ne, yadda kuka ga na rungumi kowa da kowa wani bari ne na
gudunmawar da zan iya bayarwa wajen hada da dunkulewa gami da tabbatar da Nijeriya
ta yi nasara, dukkanin Sarakunan da na gana da su, dukkanin gwamnonin da na
hadu da su, dukkanin masu ruwa da tsakin da na hadu da su a wajen taro sun
bayyana min ra’ayinsu kan batun wargaza kasa.
Don haka ina da
tabbacin wasu ‘yan kadan kuma kalilan ke wannan yekuwar kuma ba don komai suke
hakan ba illa don ra’ayinsu na kashin kai, ina da imanin cewa mu zauna gaba
daya mu tattauna kan matsalolinmu, mu ayyano su mu fito da su don yin aiki tare
wajen tabbatar da cigaban kasa da al’ummarta.
A matakin da ake cigaba
da fuskantar matsalar tsaro, yawaitar kashe-kashe, garkuwa da mutane, Jihar
Kano ta kasance mai cin gajiyar zaman lafiya a irin wannan lokacin.
Mene
ne aka yi na daban a nan ko gudunmawar Sarakuna da aka samu wannan nasarar?
Ina tsammanin kowa zai
so yin abun da Kano take yi domin hakan zai iya sanya su cikin farin ciki. Abu
mai gayar muhimmanci a nan shine muna da jajirtattun shugabanni.
Muna da gwamnati mai
kula da sha’anin tsaron jihar sosai. Ba wai sauran jihohin ma basu maida
hankali wajen amfani da dukiyarsu domin kula da sha’anin tsaron jihohin bane,
amma Gwamnan Kano yana kokarinsa sosai.
Sauran bangarorin
jama’a, da suka kunshi limamai, fastoci, sarakuna, al’umma kowa na bada nasa
gudunmawar musamman addu’o’in da ake yawan yi domin wanzuwar zaman lafiyar
jihar. Ina tunanin Allah ya amsa mana addu’o’inmu, ba wai Kano ce kawai muke
mata addu’a ba. Muna addu’a wa sauran jihohinmu da kasar ma baki daya.
Don haka ina kira ga
kowa da kowa a cikin al’umma da ya shigo a dama da shi wajen yaki da matsalar
tsaro domin lamarin ya shafi kowa da kowa. kowa da kowa ya fito ya bada nashi
gudunmawar ta addu’a, shawarwari, gabatar da tunaninsa na yadda za a hada kai
waje guda domin ganin an fito da hanyoyin shawo kan wannan matsalar na btun
rashin tsaro da ke akwai.
Abun takaici ne ka ga
mutanen da suka zauna tare tsawon sama da shekaru 60 amma sun dawo suna gaba da
juna sun zama abokan gaba.
Meye
jawo hakan?
Dole akwai wani dalilin
da ya jawo kuma ina tunanin zama tare domin duba muhimman batutuwa da suke
faruwa tabbas ta hakan matsalolinmu da daman gaske za su kai ga zama tarihi
sannu a hankali.
A lokacin ziyararka
zuwa Jihar Oyo, Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi, ya ce, shi da marigayi
mahaifinka, sun daga wa gwamnatin tarayya jijiyar wuya tare da tabbatar da
Sarakunan Gargajiya sun fara cin gajiyar kaso biyar daga cikin kudaden da ake
ware wa kananan hukumomin da suke yankunansu.
A
yanzu batun samar wa Sarakunan aikin yi a tsarin mulkin har yanzu bai tabbata
ba. Kana ganin akwai bukatar a fayyace wani aikin da za a baiwa Sarakunan a
hukumance da zai kasance daga kundin tsarin mulki?
Ina tunanin zan yi
magana kan ra’ayina na kashin kai. Abu mai muhimmanci mutum kamar Alaafin na
Oyo yana nan; marigayi mahaifina da yake Sarauta sama da shekara hamsin tare da
sauran Sarakunan da suka shafe shekaru da dama.
Idan suka ce akwai
bukatar samar da aikin yi wa Sarakuna a hukumance ni waye da zan ce a’a ko na
ja?
Ni zan yi amanna da
abun da suka gamsu da shi. Babu wani dalilin da zan yi tunanin da ya saba da
nasu a lokaci guda kuma na gamsu da cewa gudunmawar da sarakuan gargajiya ke
bayarwa kula da al’umma tare da cewa aikin kula da al’umma da jagorantarsu ma
babban aiki ne da ya ishi Basarake, don haka mu cigaba da aiki domin bunkasa
hakan, amma ina son na ce idan mafiya suka raja’a a kai da manyan magabatana
ban da wani dalili na kin amincewa.
Kwanakin baya ka
jagoranci gangamin wayar da kai kan ilimin ‘ya’ya Mata. Ta yaya kake ganin
Nijeriya da Arewa ya dace su fi maida hankali, don ganin an shawo kan wannan
matsalar na ilimin ‘ya’ya mata da kuma yawaitan yara Mata da basu zuwa
makaranta?
Batun ilimin ‘ya’ya
Mata da ma ilimi gaba daya abu ne mai gayar muhimmanci da yake neman a maida
hankali sosai a kai.
Idan kuka kalli al’umma
komai lalace; al’umma gabaki daya, daga gwamnati, sarakuna zuwa malamai, da
‘yan kasuwa, ma’aikatan gwamnati tare da daidakun jama’a.
Abubuwa dai basu tafi
yadda ya dace amma idan muka hada kawukanmu guda komai zai saukaka, fannonin
jama’a kowa ya fito a kula da fannin ilimin yara mata.
Kamar yadda na sha fadi
ne, ilimin ‘ya’ya mata na da matukar alfanu ga al’ummarmu saboda ilmantar da
diya mace kamar ka ilmantar da al’umma baki daya ne. don haka dukkanin wani
abun da muke tunanin za mu iya bada gudunmawarsa don bunkasa ilimin nan lallai ya
dace dukkaninmu mu yi.
A kan hakan mun zauna
da kungiyoyi da dama muka gana da su kan ilimin yara mata. Ina da mambar
majalisarta da ke shugabanta sashin, muna aiki tare da masu ruwa da tsaki domin
ganin yadda za a yi a bunkasa ilimi tare da magance matsalolin da suke akwai a
wananin fannin.
Muna hada kanmu da
gwamnatoci, kungiyoyi dban-daban na kasa da kasa da na cikin gida domin yadda
za a yi a bullo wa wannan matsalar.
Sannu a hankali kuma
muna kan lalubo bakin zaren magance matsalolin don haka za mu cigaba da tsage
damtse wajen ganin ilimi ya inganta.
Ta
yaya zaka sanya gwamnatin jihar ta tabbatar da samar da ayyukan yi ga matasan
da basu da aikin yi a jihar Kano?
Kamar yadda na jima ina
fadi, matsalar rashin aikin yi ba kawai a jihar Kano ne ya yi katutu ba; ba
kuma ya mamaye Arewacin kasa bane zalla, kodayake an fi kurara batun a nan.
Dukkanin abun da ke
akwai, wadannan kalubalen idan aka hadasu waje guda matsaloli da suke addabar
duniya baki daya. Tattalin arziki ya yi kasa; mutane na ta kokarin tunanin
yadda za a samar da mafita kan wannan matsalar da ke addabarmu.
Na yi magana da
gwamnati kusan kullum kan wannan batun, ba abu ne da a kowani lokaci zai fito
ina cewa na yi magana a kai ba, amma lallai kusan kullum muna fada wa gwamanti
wannan matsalar.
Na san matsayina na
Sarki wanda a kowani lokaci nake iya fada wa gwamnati bukatun jama’ata.
Zan cigaba da yin duk
mai yiyuwa wajen magana da su a kowani lokaci, basu shawarwarin da suka dace na
kuma tabbatar gwamnati za ta ke saurara tare da daukan matakan da suka dace a
kai.
Idan muka yi nazarin
halin da tattalin arzikinmu ke ciki, za mu ga yadda za mu jawo ra’ayin masu
hannu da shuni da su taimaka wa kokarin gwamnati wajen ganin an fita daga
wannan matsalar na rashin aiki yi a tsakanin jama’anmu.
No comments