Rahotanni na cewa an kashe wata matashiya a wurin zanga-zangar masu son kafa ƙasar Yarabawa yau Asabar a Jihar Legas da ke kudu maso gab...
Rahotanni na cewa an kashe wata matashiya a wurin zanga-zangar masu son kafa ƙasar Yarabawa yau Asabar a Jihar Legas da ke kudu maso gabashin Najeriya.
Wani bidiyo da aka wallafa a shafukan zumunta ya nuna gawar yarinyar rufe da wani mayafi kwance a ƙasa cikin jini.
Kazalika, wani mutum wanda babu tabbas ko shi ne yake ɗaukar bidiyon, an ji shi yana cewa harsashi ne ya kashe yarinyar a lokacin da take yin sayayya a wani shago.
Rahotanni sun nuna cewa an ji ƙarar harbin bindiga yayin da 'yan sanda ke ƙoƙarin tarwatsa mutanen.
Mutane a bidiyon na cewa shekarar yarinyar 14 da haihuwa.
Lamarin ya faru ne a wurin shaƙatawa na Gani Fawehinmi Freedom Park wanda ke kusa da inda ake zanga-zangar.
-Rahoton BBC Hausa
No comments