Rundunar sojin Nijeriya ta tabbatar da cewa an kashe Manjo Janar Hassan Ahmed na rundunar ta su. Rundunar ta sanar da cewa an kashe Jana...
Rundunar
sojin Nijeriya ta tabbatar da cewa an kashe Manjo Janar Hassan Ahmed na
rundunar ta su.
Rundunar
ta sanar da cewa an kashe Janar Hassan Ahmed ne lokacin da wasu 'yan bindiga
suka far wa motarsa a hanyar Lokoja zuwa Abuja a jiya Alhamis.
Wata
sanarwa da babban hafsan sojin Laftanar janar Faruk Yahaya ya fitar ta bayyana
cewa wata tawagar rundunar sojin ta je yi wa matar marigayin ta'aziyya.
Haka
kuma, sanarwar ta ce za a yi wa Janar Faruk jana'iza a makabartar Lungi yau
Juma'a da karfe 10 na safe.
No comments