Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta tabbatar da sace Mahmud Aliyu, Hakimin Wawa a karamar hukumar Borgu ta jihar da ake zargin ‘yan bindiga...
Rundunar
‘yan sandan jihar Neja ta tabbatar da sace Mahmud Aliyu, Hakimin Wawa a karamar
hukumar Borgu ta jihar da ake zargin ‘yan bindiga ne da aikatawa.
Jami’in
hulda da jama’a na rundunar, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin a
wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) a Minna.
Jami’in
ya ce, an yi garkuwa da Hakimin ne a daren Asabar da misalin karfe 10 na dare a
fadarsa, sai dai tuni ‘yan sanda sun fara bin sawun‘ yan bindigar don ceto
hakimin kamar yadda majiyarmu ta tabbatar.
No comments