Shugaban Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijer (MAAUN), Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya jajantawa Sanata Aliyu Wamakko, Mag...
Shugaban Jami’ar Maryam
Abacha American University ta Nijer (MAAUN), Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya
jajantawa Sanata Aliyu Wamakko, Magatakardan Wamakko bisa rasuwar matarsa,
Hajiya Atika.
Sakon ta’aziyyar na
kunshe ne a cikin wata sanarwa da Farfesa Gwarzo ya sanya wa hannu kuma aka
rabawa manema labarai a Kano a ranar Litinin.
Farfesa Gwarzo, wanda
shi ne wanda ya kafa kuma shugaban hukumar gudanarwa na Jami’ar Maryam Abacha
American University ta Nijeriya, (MAAUN), ya bayyana rasuwar Hajiya Atika a matsayin
babban rashi ba kawai ga danginta kadai ba har ma da daukacin al’ummar jihar
Sakkwato.
“Samun labarin rasuwar
matarka, Hajiya Atika ya yi matukar girgiza mu.
“A madadin iyalina da
Jami’ar Maryam Abacha American University (MAAUN), ina mika sakon ta’aziyyarmu
a gare ka bisa rasuwar matarka.
“Ina kuma so in yi
amfani da wannan dama wajen jajantawa daukacin al’ummar Jihar Sakkwato bisa
wannan babban rashi da aka yi, Allah Madaukakin Sarki ya ba ku da sauran iyalai
baki daya hakurin jure wannan rashi mara misaltuwa.” Inji Farfesa Gwarzo a
cikin sakon ta’aziyyar.
Farfesa Gwarzo, wanda
kuma shi ne Shugaban Kungiyar Jami’o’i Masu Zaman Kansu na Afrika (AAPU) ya yi
addu’a ga Allah Madaukakin Sarki da ya gafarta mata kurakuran ta, ya kuma sanya
ta a Aljannah Firdausi.
Allah ya jikanta da Rahama
ya sa ta huta, Amin.
No comments