Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Dalilin Rufe Kasuwar Da Ke 'Tara Ɓarayi Da Karuwai' A Kano

  Hukumomi a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya sun bayyana dalilan da suka sa aka rufe kasuwar Kwanar Gafan Tumatur da ke ƙarama...

 


Hukumomi a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya sun bayyana dalilan da suka sa aka rufe kasuwar Kwanar Gafan Tumatur da ke ƙaramar hukumar Garun Malam, inda suke zargin ta zama matattarar karuwai da ƴan luwaɗi da kuma ƴanfashi.

Gwamnatin Kano ta sanar da rufe kasuwar a ranar Alhamis inda ake hada-hadar kayan gwari.

Shugaban ƙaramar hukumar, Aminu Salisu Kadawa ya ce sun ɗauki matakin ne domin tsaftace kasuwar daga ayyukan baɗala.

A hirarsa da BBC ya ce an kama wani ɗanfashi ɗauke da bindiga a ɗaya daga cikin shagunan da ake kamawa ana kwana da mata masu zaman kansu.

"An kama shi da bindiga da kuma wayoyi guda 75," in ji shi.

Shugaban karamar hukumar ya ce sun ba yankasuwar wa'adi daga nan zuwa ranar 1 ga watan Janairu su fice su bar kasuwa

Ya ce za su fito da wani sabon tsari na yadda za a tafiyar da cinikayya a kasuwar, kamar samar da bangarori na sayar da kayayyaki

Ya ƙara da cewa za a samar da ɓangaren da za a sayar da dabbobi da bangaren sayar da kayayyaki kamar yadda ake yi kasuwar Yankaba.

Shugaban ƙaramar hukumar ya yi watsi da zargin cewa sun bijiro da matakin rufe kasuwar ne saboda siyasa domin ƙwace shagunan su ba magoya bayansu.

"Duk wanda gwamnati ta sayar wa shago kuma yana da takarda idan ya nuna muna za mu tabbatar masa da shagonsa sai ya ci gaba da biyan haraji," in ji shi.

Me ake zargin ana yi a kasuwar

Bisa al'ada kasuwar na ci ne a lokacin kakar kayan gwari - idan kuma suka ƙare sai a mayar da kasuwar wurin aikata baɗala, a cewar shugaban ƙaramar hukumar Garun Malam.

"Duk wani nau'i na barna da laifi duk ana gudanarwa a wannan kasuwa."

"An tsinci jarirai sabbin haihuwa da gawarwakin wasu da dama da ba za a iya tantance yawansu ba," in ji shi.

Ya ƙara da cewa wuri ne da direbobin motocin dakon kaya ke sheke ayarsu a shagunan masu kayan gwari da suke kamawa suna kwana.

"An mayar da shagunan wurin holewa, za ka ga karuwa ta kama shago,"

"Akwai kuma yan fashi da suke zuwa sakamakon kasancewar wurin matattara ce ta 'yan mata da masu zaman kansu a kasuwar," a cewar Aminu Kadawa.

Ya ce matasar ta daɗe tana damunsu kuma wannan ne dalilan da suka sa suka rufe kasuwar ta Kwanar Gafan Tumatir har zuwa lokacin da suka tsabtace kasuwar.

Ya ce za su kori dukkanin masu kama shago da ke aikata ayyukan ashsha - "Sai mun kawar da duk wani nau'i na baɗala," a cewarsa.

Ya ƙara da cewa yanzu duk wani abin da za a sayar a kasuwar sai da sanin hukumomin Garun Malam.

No comments