Daga Awwal Umar Kontagora An yi kira ga talakawan arewa da su kara hakuri kar su cire kauna ga gyaruwan kasar nan, domin siyasar ta fara z...
Daga Awwal Umar Kontagora
An yi kira ga talakawan arewa da su kara hakuri kar su cire kauna ga gyaruwan kasar nan, domin siyasar ta fara zama da gindinta. Wani mai fashin bakin harkokin yau da kullum kuma dan gwagwarmayar siyasa, Alhaji Awaisu Giwa Wanna ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Minna kan kasafin kudin sabuwar shekara na 2025 da gwamnatocin arewacin kasar suka gabatar a jahohin su.
Alhaji Awaisu, ya cigaba da cewar lokacin da turawan mulkin mallaka suka baiwa kasar nan yancin kai su tabbatar duk wani tattalin arzikin kasar nan sun yashe shi, kuma sun bar mana tsare tsaren da kafin mu iya fitar da kan mu cikin shi mun galabaita.
Arewa ita tafi bada gudunmawa wajen aza harsashen turbulan arzikin Nijeriya, ganin wadanda suka jagoranci ragamar kasar zasu warware abubuwan da aka boye aka tabbatar ba su kai labari ba, wajen anfani da marasa kishi wajen ganin an kawar da su. Sai ya zama na tsarin tafiyar mulkin kasar ya zama kashin dankali, a kowani lokaci masu mulki talakawa suke dannewa, cikin hukuncin Allah bayan sojoji sun amince da barin madafun iko, yan siyasa sun taka na su dambarwar, har aka zo mulkin Buhari, ya kammala ya sauka kuma tarihi ba zai manta irin salon mulkinsa ba, wanda dan arewa ne, kuma mafi yawan gwamnonin jahohi cikin talatin da shida, arewa na da sha tara, mun ga abubuwan da suka faru kuma ba za mu iya mantawa da su ba.
Saboda wadannan gwamnonin da ke kan mulki yanzu, ba su wuce watanni arba'in kan madafun iko ba, mun ga irin rawar da suke takawa, saboda dangane da kasafin kudaden da suka gabatar kuma ya zama doka wadanda ake tsammanin samu dan yin ayyuka da su a wannan sabuwar shekarar muna kyautata zaton zai zama mai alfanu ga jahohin su.
Amma babban matsalar da muka fi bukatar a tabbatar an kawar da shi, shi ne maganar tsaro, domin ba yadda za a samu cigaba kuma a cin ma manufa muddin ba zaman lafiya.
Kuma yan ta'addan nan na samu damar gudanar da miyagun ayyukan su ne saboda rashin hanyoyi, wanda idan ka duba kashi tis'in cikin dari na yankunan arewacin kasar nan ba sa shiguwa saboda rashin hanya. Da yadda gwamnonin mu ke da manufa iri daya na raya kasa a shekarar nan me kamawa dukkansu zasu mayar da hankalin su kan ayyukan raya kasa, samar da hanyoyi, ruwan sha, gyaran asibitoci da makarantu da arewa ta fita kunya, domin da noma kawai idan mun ajiye maganar man fetur, da sauran ma'adanan kasa, za mu iya fita kunya kuma zamu iya samar da arzikin da zamu rike kan mu.
Yau, babban birnin tarayyar kasar nan, kafin kafuwarta akwai jama'ar da ke zaune wajen an tarwatsa su, da yawan su ba su san makamar su ba, idan an samu tsaro, an samar da ilimi ga al'umma, ko ba yanzu ba za a samu wadanda zasu yi tsayin daka wajen kwato masu yancin su.
Saboda haka, ina baiwa yan uwa na talakawan arewa hakuri, da mu kara hakuri, domin ba a samun gyara rana daya, amma muna kyautata zaton hanyar da gwamnatocin arewa suka dauko indai ba su saki layi ba, lallai za a haifar da da mai ido bada jimawa ba.
Amma idan suka sake layi, wajibi ne shi ma talaka yayi abinda ya dace idan lokacin zube yazo dan tsira da mutuncin shi, amma ba a saurin wanke tukunya, tun abin dahuwa ba shigo hannu ba.
Muna kyautata zaton wannan sabuwar shekarar za ta zama ta farin ciki, da zaman lafiya a yankin arewa.
Kasar America an mulke ta, duk da cewar tafi shekaru dari biyu da kafuwa, yau ga matsayin ta, kasar Faransa ta dade tana d damawa a mulkin mallaka yau ga halin da ta samu kan ta saboda zalunci, saboda haka mu kara hakuri lokacin da zamu yi hukunci bai yi ba.
No comments