Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Wani Dalibi Ya Rasa Ransa Sakamakon Fashewar Tukunyar Gas A Minna

Daga Awwal Umar Kontagora Wani dalibi mai suna Haji ya rasu, yayin da wasu mutum uku suka jikkata, bayan wata tukunyar gas ta yi bindiga a w...


Daga Awwal Umar Kontagora

Wani dalibi mai suna Haji ya rasu, yayin da wasu mutum uku suka jikkata, bayan wata tukunyar gas ta yi bindiga a wajen wani mai gyaran taya a Minna.

Lamarin ya faru ne a ranar laraba, kusa da ofishin ’yan sanda da ke Kpakungu cikin garin Minna .

Mai gyaran tayar mai suna Mohammed da É—ansa, da wani É—alibi sun samu munanan raunuka a lokacin da tukunyar ta fashe, yayin da Haji ya rasu nan take a wajen.

Shaidu sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1 na rana, lokacin da mai gyaran tayar yake gyara wasu tayoyin manyan motoci.

Fashewar ta lalata shagonsa tare da rushe katangar wani gida da ke kusa da wajen.

Wani mazaunin yankin, Usman Muhammad, ya bayyana cewa karar fashewar ta tayar da hankalin jama’a.

Ya kara da cewa an yi jana’izar marigayin Haji a makabartan Kpakungu.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce wadanda suka  jikkata an garzaya da su asibiti. Amma, abin takaici, daya daga cikin daliban ya rasu, yayin da sauran suke samun kulawa. 

No comments