Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Neja ta yabawa Ƙungiyar Hajj Da Umrah Bisa Jajircewar Ta Wajen Faɗakar Da Maniyyatan Jihar

Daga Awwal Umar Kontagora   Gwamnatin jihar Neja ta yabawa ƙungiyar Hajj and Umrah Trainers Association bisa jajircewar ta wajen...


Daga Awwal Umar Kontagora 

Gwamnatin jihar Neja ta yabawa ƙungiyar Hajj and Umrah Trainers Association bisa jajircewar ta wajen fadakar da kan maniyyatan jihar.  Shugaban hukumar jin dadin alhazai ta jihar Neja,  Sheikh Abubakar Muhammad Rabi'u Beji ne yayi yabon a ta bakin daraktan gudanarwar hukumar, Malam Attahiru Dukku, lokacin wani taron da kungiyar ta shiryawa mambobinta a dakin taron hukumar kan shirye shiryen aikin Hajji da Umrah mai zuwa.

Taron dai ya gudana Littinin din makon nan,  tunda farko a bayanin shugaban hukumar yace hukumar yanzu haka hukumar ta fara karban kudaden maniyyatan bana, naira miliyan takwas da dari hudu a matsayin ajiya ta hannun bankunan Ja'iz,  da WEMA da Polaris.

Dukku, ya jawo hankalin malaman a wajen fadakar da al'umma,  su shaida ma duk wani mai sha'awar biya ma wani musamman Dattijo mai shekaru su tabbatar sun hada da wanda zai kula da dattijon koda mahaifansu ne ko dan uwa. 
Aikin Hajji ba karamin abu ba ne da za a bar maniyyaci na wahala. 

Da yake tsokaci bayan fara taron, shugaban kungiyar a jihar Neja,  Sheikh Muhammadu Liman Masha'Allahu, ya baiwa yayan kungiyar hakuri kan abinda ya faru a shekarar da ta gabata,  na rashin samun kujera dan rakiyar mahajjata zuwa kasa mai tsalki kamar yadda aka saba. 
Masha'Allahu, yace mun zauna da hukumomi mun kuma tattauna da su,  sun tabbatar mana da cewar duk da cewar kungiyar mu,  kungiya ce mai zaman kan ta,  da yardar Allah a wannan shekarar za a ga sauyi sabanin abinda ya faru a shekarar da ta gabata. 

Shugaban ya cigaba da cewar duk wanda yace zai yi koyi da Manzon Allah tabbas sai ya ga jarabawa, dan haka kamar yadda hukumar jin dadin alhazai ta fadi ne,  wannan aikin ba na biyan wani hasafi ba ne ko jiran sakamako daga wani aiki ne da muka kudurci aiwatar da shi saboda Allah, dan haka za mu kaira kaimi wajen bada lokuttan wajen aiwatar da wannan hidimar da muka kallafawa kan mu saboda Allah. 

Abin da ya faru a shekarar da ta gabata na rashin samun wakilcin kungiyar mu ga alhazan da su sauke farali ba kasawa ba ne,  kuma hakan ya dada kara likkafar kungiyar mu gaba. Dukkanin kananan hukumomin jihar nan muna da jimlar adadin maniyyatan da suka tafi sauke farali a bara,  kuma wani babban nasarar da muka samu shi ne, irin horon da muka baiwa maniyyatan jihar nan sun bi kuma sun yi aiki da shi,  dan haka ba wani rahoton da ya fito na kasawa ko aikata wani abinda ba daidai ba ga maniyyatan jihar Neja a bara. 

Muna kara jadaddawa ga mahukuntan jihar nan na nuna goyon baya da kyawawan addu'ar alkhairi gare su, bisa goyon bayan da suke baiwa wannan kungiya. 

Liman Masha'Allahu, ya nemi malamai na sassan sauran kananan hukumomi da su hada kai da jami'an da ke kula da tattara bayanan maniyyata domin yin aiki kafada da kafada wanda hakan zai saukaka wajen hada maniyyatan wuri daya dan daukar horo kamar yadda ya dace. 

Abu Sufyan Ahmad Siri-siri, shi ne shugaban APOW na yankunan kananan hukumomin jihar Neja,  yace su da malamai masu fadakar da maniyyatan jihar aikinsu yana tafiya daidai, domin suna da kyakkyawar fahimta,  don haka duk wani gudunmawa da kungiyar nan ke bukata za mu tabbatar mun bada shi. 
Sai yace malamai su ji tsoron Allah,  aikin nan da suka sanya gaba aiki ne maigirma,  dan haka su tabbatar dukkanin horon da zasu bayar ya zamo bai daya,  abinda aka gudanar a karamar hukumar Chanchaga,  ya zama irin shi ne a Bargu,  Mashegu da dukkanin bangarorin kananan hukumomin jihar. 

Siri -siri,  ya yabawa shugabancin kungiyar bisa kokarin hada kan malamai lungu da sakon yankunan kananan hukumomi na ganin an tafi bai daya. 

Hukumar jin dadin alhazan jiha dai ta bayyana cewar yanzu haka ana cigaba da karban kudaden maniyyatan bana, wanda ake sa ran rufawa ranar bakwai ga watan janairun nan mai zuwa.

No comments