Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Za a ƙaddamar da sabon gidan Talabijin a Zariya

Daga Ammar M. Rajab   Za a ƙaddamar da sabon gidan Talabijin mai suna Arewa Vision TV a garin Zariya ta jihar Kaduna.  Mamallaki...

Daga Ammar M. Rajab 

Za a ƙaddamar da sabon gidan Talabijin mai suna Arewa Vision TV a garin Zariya ta jihar Kaduna. 

Mamallakin gidan Talabijin ɗin, Malam Alhaji Aminu Yusif Mamman D shi ne ya bayyanawa wakilinmu a Zariya. 

Sanarwar ta ci gaba da cewa taron zai gudana ne a gobe Laraba 1 ga watan Janairun 2025 a harabar gidan Talabijin ɗin dake bayan ginin Nakwama dake titin Sokoto kusa da Al-Nasiha Restaurant dake garin Zariya ta jihar Kaduna. 

Arewa Vision TV tasha ce ta zamani da aka buɗe domin yaɗa labarai da rahotanni domin ci gaban al'umma, faɗakarwa da kuma kare ƴancin bil'adama. 

Ana sanar da al'umma cewa tashar ta tanadi shirye-shirye daban-daban da suka shafi ci gaban al'umma tare da zaburantar da su. Kuma za a iya kama tashar a Satilayet kamar haka: F=12538, S=05000, Nigocomsat, P=H. 

Gidan Talabijin na Arewa Vision ya yi alƙawarin kasancewa mai ƙima a fagen yaɗa labarai a Zariya da ma duniya baki ɗaya wajen inganta ci gaba da wayar da kan al'umma.

No comments