Daga Awwal Umar Kontagora An yi kira ga al'ummar musulmi da su kawar da bambance bambancen da ke tsakaninsu tare da yin ri...
Daga Awwal Umar Kontagora
An yi kira ga al'ummar musulmi da su kawar da bambance bambancen da ke tsakaninsu tare da yin riko da koyarwa Annabin Rahama wajen zaman lafiya da bunƙasuwar arziki.
Mai girma Sheshi Katcha, Alhaji Baba Umar Adamu ne ya yi kiran a lokacin kammala zagayen Mauludin Manzon Allah, karo na goma sha biyu da gundumar masarautar ke shiryawa.
Sheshi, ya cigaba da cewar Manzon Allah ne yazo da sallah, domin shi ya karbo kuma ya koyar da mu yadda za mu gabatar da shi. Ya ce; mu a Katcha mun zabi fifita bukin Mauludin Allah ne akan bukukuwan idi da jama'a suka saba da shi.
"Zan yi anfani da wannan damar kamar yadda na saba, wajibi ne al'ummar musulmi da su hada kai, wajen kyautata mu'amalarsu da juna har da waÉ—anda ba musulmi ba, domin addinin musulunci ya horar da mu yadda za mu gudanar da rayuwar mu, mu'amalar mu da abokan zama.
"Yau duk inda ka zagaya a garin Katcha za ka fahimci jama'a na cikin farin ciki, donin akwai abu mai muhimmanci da suke nuna shaukin su akan shi", ya lurantar.
Alhaji Muhammad Mohammad Danjuma Bangi, shi ne shugaban kwamitin shirya Mauludin na bana, ya ce a shekaru sha da fara wannan tsarin a kullum sai ka ga abin burgewa.
"A bara ni kaina na kashe sama da miliyan biyu a cikin aljihuna kawai saboda murnar wannan ranar, a bana kuma da aka ba ni damar jagorantar shirya wannan bukin mun zo da wani tsari na daban, na ganin lungu da saƙo mun wadata al'umma da abinci da ruwan sha, ta yadda duk bakon da yazo don taya mu murna, ko ganewa idonsa irin hidimar da mu ke yi bai tagayyara ba.
"Mun zabi wannan lokacin na kakar abinci, lokacin da muka tabbatar mun kammala aikin gona na daminar da mu ka yi, dan nuna godiyar ga Allah ta hanyar nuna farin cikin mu da samuwar Manzon Allah.
Duk wani haifaffen garin nan, idan ma uzuri ya hana shi halartar wannan bukin to ka tabbatar ya aiko da gudunmawar sa. Saboda mu a gundumar Katcha, bukin mauludin Manzon Allah yafi buki idi muhimmanci a wurin mu", ya tabbatar.
Sheikh Isah Danjuma Katcha, É—aya daga cikin dattijai kuma manyan malaman gundumar da ya yi sharhi tare da nuna alfanun wannan bukin.
Sheikh Danjuma, ya ce Manzon Allah ( S.A.W) shi yazo muna da sallah a matsayin wani ginshiki na neman kusanta zuwa ga Allah, ka ga da ba a samar da shi ba, da ba mu san halin da muke ciki ba. To idan ka fifita wannan ranar a matsayin ranar nuna farin cikin ka ba kai laifi ba.
Malamin ya cigaba da cewar yau abin bakin ciki da takaici, wani musifa da ya aukawa al'umma, shi ne fifita waliyai akan Manzon Allah, a cikin Tijjaniya, ka ji Batijjane na kwatanta matsayin Manzon Allah da Shehu Ahmadu Tijjani, wanda shi wanda muke koyi da shi ma yana koyi ne da Manzon Allah.
A cikin littafinsa yake cewa idan ya fadi abu ka binciki Al-kur'anin da Hadisin Manzon Allah, idan ka ga ya saba to ka ajiye na shi ka rungumi wanda ka samo a cikin Al-kur'anin girma ko na Hadisin Manzon Allah, shi fa ke nan bai kwatanta matsayin sa da Manzon Allah, sai kai mabiya, wannan akwai kuskure babba.
Sheikh Danjuma, ya yabawa malamai da shugabannin gundumar wannan masarautar na yarda da hadewa dan raya wannan rana ta haihuwar fiyayyen halitta, wanda yazo da alkhairan da zasu kai al'umma ga tsira.
Fa'idarsa, shi ne zumunci, soyayya, tare da nuna farin ciki da samuwar Manzon Allah. Yace wani abin burgewa, duk yadda ka ke ganin sabani ko rashin fahimta da tsakanin wasu da ranar nan tazo sai ka ga sun hade an yafewa juna, an ci abinci tare an yi raha tare da samun karin ilimi na irin bayanan da malamai kan yi mana irin wannan ranar cikin farin ciki da soyayya ga junan mu.
Masarautar gundumar Katcha, da ke karkashin masarautar Bida, wadda mai Nupe, Etsu Dakta Yahaya Abubakar ke jagoranta, tana da masarauta a matsayin gunduma da ake kira da sunan SHEHI, Sheshi shi ke jagoranta masarautar wadda ke karkashin karamar hukumar Katcha.
Ta shahane a bangaren noma da kamun kifi, wadda Allah ya albarkace da ruwa ta hannun babban tafkin Kainji, wadda ke da iyakoki da kananan hukumomin Agaie a bangaren yamma, Lapai da ke bangaren Arewa, sai Bida a bangaren Kudu.
Ta shahara a karban baki, musamman daga sassan jahohin kasar nan, da kasashe makotan Nijeriya, masu safarar kayan abinci da noma, wadda ke da babbar kasuwar da ke ci ranar juma'a, amma duk da kasancewarta lungu, madatsar ruwan Baro da gwamnatin tarayya ke yunkurin samar da tashan jiragen ruwa da yin safara akan ruwa daga yankin Kudu zuwa arewacin kasar da ke karkashin karamar hukumar Agaie ta kara fitar da wajen kara karban baki masu sha'awar noma da sayen kayan anfanin gona, da saye da sayar da kifi.
Gundumar Katcha, tana zagaye da wasu kauyuka da ke bakin ruwa wadda kusan itace babban birnin da ba a iya tafiyar da rayuwa a yankin sai an mannu da ita.
Kan haka ta ware unguwa guda a tsakiyar garin da ake cewa KWATA, wannan unguwar kusan nan ne matattara kuma cibiyar gudanar da kasuwanci a garin.
Alhaji Baba Umar Adamu shi ne Sheshi kuma jagoran kula da wannan yankin baki dayan ta, wadda asalin wadanda suka kafa gundumar tun asalinta Nupawa, hakan bai hana baiwa baki da sauran kabilu damar mike kafa dan neman arziki ba.
Duk da kasancewarta mai arzikin kasar noma da kamun kifi, bai hana ta shahara wajen ilimin boko da siyasa ba, tana kan gaba wajen bada kuri'u a lokacin zaben shugabannin siyasa a matakin jiha da tarayya.
No comments