Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sanata Yari Ya Ce Ɗaukar Sojoji Akai-akai Zai Sanya Kashi 85 Na Manoma Su Yi Noma Domin Magance Matsalolin Arewa

Daga Hussaini Yero  Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanatan Zamfara ta yamma, Abudulaziz Yari ya tabbatar da cewa, ɗaukar sojoji d...


Daga Hussaini Yero 

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanatan Zamfara ta yamma, Abudulaziz Yari ya tabbatar da cewa, ɗaukar sojoji da gwamnatin tarayya ke yi a duk bayan wata shida zai taimaki manoma kashi 85 su noma gonakin su a damina mai zuwa da yardar Allah. "Kuma waɗannan sojoji za a turo su lungu da saƙo a faɗin ƙasar nan don ba al'umma kariya wajen tafiyar da rayuwar su".

Sanata Yari ya bayyana hakan ne a taron manema labarai da ya yi a yau Asabar a Talatan Mafara.

A taron manema labaran Sanata Yari ya tabbatar da cewa, shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya tabbatar masu a majalisa lokacin da ya kai kasafin kudi na 2025, cewa babu babban abin da ke cim masa  tuwo a ƙwarya irin rashi samun kwanciyar hankali a ƙasar nan. A don haka da yardar Allah zai yi duk abin da ya kamata akan smar da tsaro.

Sanata Yari ya yi kira ga ƴan Jam'iyyun adawa da su daina alaƙanta rashin tsaro da mulkin jam'iyyar APC, don wannan rashin tsaron tun mulkin jam'iyyar PDP na ya ke. 

Kuma ya yi kira ga al'ummar ƙasar nan da su ci gaba da yin addu'a don samun dawamammen zaman lafiya a ƙasar mu baki ɗaya.

No comments