Daga Hassan Ibrahim A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne 21 ga watan Disamba na wannan shekara, Jaridar Taskira ta karrama Iyalan...
Daga Hassan Ibrahim
A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne 21 ga watan Disamba na wannan shekara, Jaridar Taskira ta karrama Iyalan marigayi Alhaji Sani Umar wanda ya samar da Sani Umar Metal Construction and International Security Doors, da ke tsohuwar Panteka cikin garin Kaduna, bisa irin gudunmuwar da ya bayar na cigaban al'umma a cikin zamantakewa na rayuwa.
A jawabinsa jim kaɗan bayan amsar lambar yabon ɗaya daga cikin iyalan Marigayin Mu'azu Ibn Nasir ya bayyana cewa abun farin ciki ne da jin daɗi ga iyalan Marigayin kasancewar al'umma suna alfahari da shi bayan bashi a doron ƙasa.
Ya na mai cewa akwai abubuwa da dama da basu sani ba game da mahaifin nasu, kasancewar dukkan abinda ɗan Adam ke aikatawa a bayyane ne ko a ɓoye al'umma zasu gano shi bisa ƙudirin sa na alkhairi da kyakkyawar mu'amalar sa da al'umma.
Inda yi yi kira ga al'umma wajen kyautata mu'amala a zamantakewa na rayuwa tare da aiwatar da kowane abu saboda Allah kasancewar yin hakan sakayyar mutum na wajen Allah SWT.
Mu'azu ya kuma yi kira ga matasa wajen koyi da mutanen kirki tare da jajircewa wajen neman ilimi da kuma sana'a domin samun abinda zasu dogara dashi a rayuwa.
Tun farko a ke jawabin sa Manajin Direkta na Jaridar Taskira, Alhaji Yusuf Abdullahi wanda ya samu wakilcin Babban editan Jaridar Mustapha Abubakar Kajuru ya ce "duk da cewa mun kira irin wannan taro da sunan karramawa to amma kai tsaye ba karramawa Jaridar Taskira take yi ba sai jaddadawa saboda ina da tabbacin cewa mafi yawan mu da ke wannan wuri Allah da kansa ya gama dukkan wata karramawa a gare mu."
"Idan haka ne za a yarda da ni cewa wannan rana - rana ce da wannan Jarida ta ware domin jaddadawa, ƙarfafawa wasu bayin Allah don ƙara musu kwarin gwiwa akan ƙoƙarin da kowannen su ke yi a ɓangaren aikinsa ko sana’ar sa."In ji shi.
No comments