Gwamnatin jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya, ta ƙaddamar da shirin rabon tallafin kuɗi ga masu ƙaramin ƙarfi a jihar. Shirin...
Gwamnatin jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya, ta ƙaddamar da shirin rabon tallafin kuɗi ga masu ƙaramin ƙarfi a jihar.
Shirin - wanda gwamnan jihar, Ahmad Aliyu ya ƙaddamar ranar Juma'a a birnin Sokoto - na da aniyar tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi domin rage talauci a cikin al'umma.
Yayin da yake jawabi a wajen ƙaddamar da shirin, Gwamna Ahmad Aliyu ya ce shirin na daga cikin jerin shirye-shiryen bayar da tallafi domin dogaro da kai da gwamnatinsa ta ɓullo da su.
''A yau ma za mu kafa sabon tarihi, inda za mu fara raba kuɗin tallafi domin dogaro da kai ga masu ƙaramin ƙarfi. Kimanin mutum 9,700 za su rabauta da wannan tallafi a wannan karo, inda wasu za su samu naira 75,000 wasu kuma naira 100,000 yayin da wasu samu samu naira 150,000'', in ji gwamnan.
Ya ƙara da cewa ''Mun bayar da wannan tallafi ne domin ƙarfafa wa jama'a gwiwa don fara sana'o'in dogaro da kai''.
Haka kuma Gwamnan ya yi kira ga mutanen da suka amfana da tallafin da su yi amfani da kuɗin ta hanyar da ta dace, wajen kafa sana'o'in dogaro da kai domin su tallafi kawunansu.
No comments