Shugaban na mulkin sojin Nijar ya ce daga bayanan da suka samu a daÉ—ewa sun fahimci cewa na shirin kafa sansanin Lakurawa a wani daji da ke ...
Shugaban na mulkin sojin Nijar ya ce daga bayanan da suka samu a daÉ—ewa sun fahimci cewa na shirin kafa sansanin Lakurawa a wani daji da ke jihohin Sokoto da Zamfara da kuma Kebbi.
''Wasu manyan 'yanta'adda da muka kama, sun shaida mana cewa a ranar 4 ga watan Maris ɗin shekarar 2024, Faransa ta ƙulla wata yarjejeniya da mayaƙan ISWAP, kuma shugabannin Najeriya na sane da ita, cewa za a mayar da dajin Gaba da ke jihohin Sokoto da Zamfara da Kebbi a Najeriya sansanin horas da mayaƙan Lakurawa'', in ji shugaban na Nijar.
Janar Tchiani ya yi zargin cewa an tanadin sansanin ne domin horas da mayaƙan Lakura don su watsu a jihohin Sokoto da Zamfara da kuma jihar Kebbi da kuma jamhuriyar Nijar.
Shugaban na Nijar ya ce duk da iƙirarin mayaƙan da suka kama suka na cewa jagororin Najeriya na sane, ba su yarda da maganar 'yan bindigar ba.
Haka ma shugaban na Nijar ya zargi mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu da masaniya game da wannan batu.
Yayin zargin cewa an ƙuduri aniyar horas da Lakurawan ne domin su kawo tarnaƙi ga aikin bututun man ƙasar da ka shimfiɗa zuwa Jamhuriyar Benin mai makwabtaka.
Janar Tchiani ya zargi ƙasashe makwabtan Nijar da bai wa Faransa damar kafa sansanoni a ƙasashen domin horas da 'yanta'adda da niyyar yaƙar Nijar.
A baya-bayan nan dai dangantaka tsakanin Najeriya da Nijar na ci gaba da yin tsami, ko a makon da ya gabata ma gwamnatin mulkin sojin Nijar ɗin ta zargi Najeriya da shirya mata maƙarƙashiya, kodayake gwamnatin Najeriya ta musanta zargin.
No comments