Daga Hussaini Yero Mataimaki na musamman na Jam’iyyar APC ta kasa kuma mai bada shawara kan shari’a Kabiru Oro Kaura Namoda, ya yabawa sh...
Daga Hussaini Yero
Mataimaki na musamman na Jam’iyyar APC ta kasa kuma mai bada shawara kan shari’a Kabiru Oro Kaura Namoda, ya yabawa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu bisa sake nada Fatima Umaru Aliyu Shinkafi a matsayin Sakatariyar Babban Asusun Raya Ma’adinai, inda ya ce nadin nata. ya abun ayaba ne ga Shugaban Kasa.
Mataimaki na musamman na kasa na bada shawara kan harkokin shari’a Kabiru Oro Kaura Namoda ya bayyana haka ne ga manema labarai.
A cewar sa Hajiya Fatima Umaru Aliyu Shinkafi ta nuna jajircewarta wajan ganin acigaban Ayyuka na shugaban kasa Bola Tinubu.
"Mu matasa 'yan asalin Kaura Namoda masu goyon bayan APC munyi matukar godiya ga Allah da ya ba Hajiya Fatima Umaru Aliyu Shinkafi,wannnan babban mukami muna farin ciki da cikakken goyon bayan ga Shugaba Tinubu da gwamnatinsa."
“Saboda haka mun godewa shugaban kasa Tinubu kan wannan karimcin tare da ba shi tabbacin ci gaba da goyon bayan mazabar Fatima Umaru Aliyu Shinkafi ga gwamnatin sa”.
"Matasan APC daga Fatima Shinkafi a mazabar Zamfara ta arewa sun yaba wa shugaban Kasa bisa sake nada mace da ba ta da kura-kurai don gudanar da SMDF/PAGMI".
Kabiru Oro ya ci gaba da cewa, Hajiya Fatima Umaru Aliyu Shinkafi ta tashi tsaye wajen tallafawa al’ummar mazabarta, da jihar Zamfara musamman a lokutan bukukuwa.
"Wannan ya nuna cewa ita mai goyon bayan APC ce, kuma mai bin dimokuradiyya ta gaske tare da mutunta mutane a koda yaushe.
Dan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya fara nada Fatima Shinkafi a wannan aiki, kuma tana daya daga cikin wadanda suka kawo sauyi a fannin ma’adanai a kasar nan.
Shugaba Bola Tinubu ya sanar da sake nada Hajiya Fatima Umaru Shinkafi a matsayin babbar sakatariyar asusun bunkasa ma'adanai watau (Solid Minerals Development Fund/Presidential Artisanal Gold Mining Initiative (SMDF/PAGMI).
No comments