Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sojoji Sun Ce Sun Kashe Ƙasurgumin Ɗanbindiga Ma'oli A Zamfara

  Sojojin birged na 1 na dakarun Operation Fansan Yamma, sun kashe wasu ƴanbindiga, ciki har da wani ƙasugumi, Alhaji Ma'oli, a ranar 26...

 


Sojojin birged na 1 na dakarun Operation Fansan Yamma, sun kashe wasu ƴanbindiga, ciki har da wani ƙasugumi, Alhaji Ma'oli, a ranar 26 ga Disamban 2024.

Sojojin sun kai farmakin ne a ƙauyen Mai Sheka, kusa da garin Kunchin Kalgo, inda Ma'oli ya daɗa yana ƙuntata wa jama'a ta hanyar ƙaƙaba wa mazauna Unguwar Rogo da Mai Sheka da Magazawa da yankin Bilbis da ke ƙaramar hukumar Tsafe haraji.

Kakakin jami'an tsaron haɗin gwiwar, Abubakar Abdullahi ya ce kashe Ma'oli ya jefa farin ciki a zukatan mutanen yankin.

Sojojin sun kai farmakin ne bayan samun bayanan sirri kan harkokin ƴanbindiga a yankin Bilbis, wanda hakan ya sa sojojin suka kai ɗauki, suka samu nasarar ɗakile yunƙurin ƴanbindigar.

No comments