Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed ya yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da ya dakata da batun gyare-gyaren haraji da ya ɗauko. Ya bayyan...
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed ya yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da ya dakata da batun gyare-gyaren haraji da ya ɗauko.
Ya bayyana haka ne a ranar Alhamis lokacin bikin Kirsimeti da ya shirya wa al'ummar Kirista a jihar.
Ya ce ƙudurorin ba za su yi wa ƴan arewa kyau ba, inda ya ce gwamnoni ba za su iya biyan albashi ba.
Ya ce, "ƙudurorin haraji ba za su amfani arewacin Najeriya ba. Dole su saurare mu, idan ba su saurare mu ba, ke nan an koma kama-karya, kuma hakan ba shi da kyau.
"Bai kamata su yi ƙudurori da za su amfani jiha ɗaya ba kawai. Ba wai maganar addini ko ƙabilanci ake ba, magana ce ta haɗin kan ƙas," kamar yadda Channels ta ruwaito.
Ya ƙara da cewa za su cigaba da matsa lamba domin a yi abin da ya dace, "amma idan suka ƙi, ba za su ƙi gani ba. Za mu yaƙi lamarin."
No comments