A jiya Talata 28 ga watan Afrilun 2021, labarai marasa dadin ji sun auku a sassan Nijeriya na kai hare-hare da kashe jami'an...
A jiya Talata 28 ga watan Afrilun 2021, labarai marasa dadin ji sun auku a sassan Nijeriya na kai hare-hare da kashe jami'an tsaro da ke bai wa kasarnan kariya.
Jaridar MADOGARA ta tattaro wasu daga cikin hare-haren nan da aka kai cikin awa 24, wanda ya yi sanadin mutuwar jami'an tsaro 21.
1. A jihar Kebbi wadansu'yan bindiga sun kashe jami'an 'yan sanda guda 8.
2. A jihar Imo an kashe 'yan sanda guda biyu.
3. A jihar Ribas kuwa ana kashe sojoji guda biyar.
4. Inda a jihar Binuwe kuma aka kashe 'yan gudun hijira guda 7.
5. A jihar Ebonyi kuwa, an cinnawa babbar Kotun Tarayya wuta ne.
6. An tabbatar da cewa Boko Haram ta kwace karamar hukuma daya a jihar Neja.
7. An kuma kashe da dama a wadansu kauyukan jihar Katsina.
No comments