Kungiyar Malaman kiristoci ta ‘Christian Bishops and Clergy Council’ ta nuna goyon bayanta ga shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa go...
Kungiyar Malaman kiristoci ta ‘Christian
Bishops and Clergy Council’ ta nuna goyon bayanta ga shugaban kasa Muhammadu
Buhari bisa goyon bayansa ga ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr
Isa Ali Pantami bisa zargin ministan da goyon bayan ta’addanci a shekarun baya.
Kungiyar ta bayyana goyon bayanta ne
a gangamin da ta shirya a dandalin neman ‘yanci na Unity Fountain dake birnin
tarayya Abuja. Inda suka bayyana cewa wadanda suke daukar nauyin zargin
ministan wadansu kusoshi ne da canje-canjen da ministan ya kawo ya shafe su.
Malaman kiristocin sun kasance suna
dauke da takardu da kwalaye da suka daga wanda suke rubuce-rubucen goyon
bayansu ga shugaba Buhari tare da bayyana shi a matsayin shugaban da ya hada
kan kasa.
Kungiyar ta jaddada cewa shugabannin
kiristoci sun gudanar da gangamin ne domin nuna goyon bayan su da tattauna
zaman lafiya domin samun hadin kan kasa da kuma nuna goyon baya ga shuganni a
kasar.
Da yake jawabi a wurin gangamin,
shugaban kungiyar Bishop Abel King ya ce fitowarsu ya zama dole ne sakamakon
yadda suka ga kowa na bayyana ra’ayinsa kan zargin ministan.
No comments