Rahoton BBC HAUSA Majalisar dattawan Najeriya ta ce za ta nemi ta zauna da shugaba Muhammadu Buhari a madadin sanatoci 109 saboda ha...
Rahoton BBC HAUSA
Majalisar dattawan Najeriya ta ce za
ta nemi ta zauna da shugaba Muhammadu Buhari a madadin sanatoci 109 saboda
halin da tsaro yake ciki a ƙasar.
Ta ce buƙaci manyan hafsoshin tsaron
kasar su gaggauta tura sojoji domin kare iyakokin yankunan da ke fama da
matsalolin tsaro.
Majalisar ta yanke wannan shawarar
ce bayan zamanta na yau Talata wanda a ciki Æ´an majalisar suka bayyana damuwa
game da halin da tsaro yake ciki a kasar.
A cewar majalisar, akwai bukatar a
hanzarta kafa sansanin soja da na yan sanda na din-din-din a kusa da kananan
hukumomin Shiroro da Rafi da ke jihar Neja.
Kafin majalisar ta É—auki wannan
matakin, Sanata Olubunmi Adetunmbi ya ce la'akari da ƙaruwar hare-hare a sassan
ƙasar, akwai buƙatar a yi ganawar sirri da shugaba Muhammadu Buhari domin kawo
maslaha mai É—orewa game da lamarin da ya zama abin kunya.
Ya bayyana haka bayan da abokin
aikinsa Sanata Sani Musa ya yi nuni da dokar majalisar ta 42 da 52 da ta nemi
majalisar ta gabatar da ƙudiri kan ayyukan ƴan bindiga da mayakan Boko Haram a
kananan hukumomin Shiroro da Rafi da ke jihar Neja - lamarin da ya dauki wani
salo na daban.
Sai dai a cewar Sanata Adetunmbi,
matsalar tsaron ba wai Neja ta shafa ba, abu ne da ya shafi ƙasar baki ɗaya.
A ganinsa, abin da ke faruwa a
Najeriya lamari ne da ka iya juyewa zuwa yaƙi saboda a cewarsa, "cikin
shekara 10 da ta gabata, akwai rahotanni da dama da suka nuna cewa Najeriya na
iya shiga halin da take ciki a yanzu".
Shi kuwa Sanata Ajibola Basiru da ke wakiltar Osun ta tsakiya cewa ya yi rundunar yan sandan kasar ta gaza tabbatar da tsaro a kasar a don haka yake ganin akwai buƙatar a bijiro da tsare-tsaren da za su magance matsalolin tsaro a Najeriya.
Ya ce akwai buƙatar a ɗibi jami'an
tsaro kimanin dubu biyar a kowace jiha.
No comments