A jiya Litinin 26 ga watan Afrilun 2021, labarai marasa dadin ji sun faru a sassa daban-daban na kasarnan. Ga labarai takwa...
A jiya Litinin 26 ga watan Afrilun 2021, labarai marasa dadin ji sun faru a sassa daban-daban na kasarnan.
Ga labarai takwas da MADOGARA ta tattaro muku;
1. 'Yan bindiga sun sake kashe dalibai biyu cikin daliban Jami'ar Greenfield dake jihar Kadun da suka sace.
2. Wadansu 'yan bindiga sun sace dalibai da dama a Jami'ar Gona ta gwamnatin Tarayya dake Makurdi a jihar Binuwe.
3. Rundunar sojin sama ta yi wa rundunar sojin kasa luguden wuta bisa 'kuskure' a garin Mainok ta jihar Borno. Inda ta kashe da daman gaske.
4. Boko Haram sun kafa tutoci a garin Kaure ta jihar Neja. Inda gwamnan jihar ya ce kiria ya rage su shiga birnin Tarayya Abuja.
5. 'Yan bindiga sun kashe dalibai Tara a dakin kwananansu a garin Igbariam dake jihar Anambra.
6. Boko Haram sun farmaki garin Gwoza ta jihar Borno.
7. 'Yan bindiga sun kashe matafiya uku a jihar Osun.
8. Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta tabbatar da kashe wani DPO da jami'ansa takwas a Jihar Kebbi.
No comments