Gwamnatin Nijeriya ta maida martani a fusace game da bude hedikwatar kafar sada zumunta ta Twitter na Afirka da ta yi a Ghana duk da c...
Gwamnatin Nijeriya ta maida martani a
fusace game da bude hedikwatar kafar sada zumunta ta Twitter na Afirka da
ta yi a Ghana duk da cewar Nijeriyar ta zarta Ghana a yawan masu amfani da
Twitter kamar yadda rahoton DW Hausa ya tabbatar.
Gwamnatin Nijeriya dai ta fusata da
ma harzuka inda ta kai ga nuna bacin ranta a kan wannan mataki da kafar sada
zumunta ta Twitter ta dauka na bude hedikwatarta a kasar Ghana maimakon
Najeriyar wacce take da masu amfani da shafin har milyan 25 in aka kwatanta da
mutane milyan takwas da suke amfani da Twitter a Ghana.
Minsitan yada labaru da al’adun gargajiya na Nijeriyar
Lai Mohammed ya dora laifi ga mutanen da ya kira marasa kishi musamman
matasan da suka yi mumunanr zanga-zangar nan ta nuna bacin ransu a kan zargi na
cin zarafin ‘yan sanda.
An dai faro zanga-zangar nuna kyama ga cin
zarafin jama’a da ake zargin ‘yan sandan Nijeriyar da aikatawa ne ta kafar sada
zumunta ta Twitter kafin matasan suka fito fili, su nuna ‘yar yatsa a
kansu na cewa su suka jawo Nijeriya.
Dalilan Twitter Na Kafa Cibiyarta A Ghana A Maimakon Nijeriya
No comments