Daga Hussaini Ibrahim Gusau Dauda Lawal Dare, ya lashe zaben fidda gwamni na takarar kujerar gwamna na jamiyyar PDP a Zamfara, ...
Daga Hussaini Ibrahim Gusau
Dauda Lawal Dare, ya lashe zaben fidda gwamni na takarar kujerar gwamna na jamiyyar PDP a Zamfara, da kuri'a Dari hudo da talatin daya.
Jami'in kula da zaben Ambasada Adamu Maina Waziri, ya bayyana haka jim kadan bayan kammala zaben a Hedikwatar jamiyyar ta jiha da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara.
Ambasada Waziri ya kara da cewa, 'yan takara hudo ne suka tsaya takara, wanda suka hada da, Eng, Ibrahim Shehu wanda ya samu kuri'a biyar. Sai kuma Wadatau Madawaki ya samu kuri'a uku, sai kuma Hafiz Usman Nahuce bai samu kuri'a ko daya ba, sai kuma Dauda Lawal Dare ya samu kuri'a dari hudo da talatin da daya. Inji Ambasada Waziri Maina.
Tunkafin lokacin fara kada kuri'a , sai 'yan takara uku suka fice daga ofishini jamiyyar PDP, suka janye Daligetdin su da sunan zaba'ayi masu adalci.
'Yan takara da suka kaurace ma zaben sun hada da, Eng. Ibrahim shahe da Hafiz Usman Nahuce da Wadatau Madawaki.
No comments