Daga Hussaini Ibrahim, Funtua Zaben fidda gwani na jamiyyar PDP a mazabar Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Katsina ta kudu, D...
Daga Hussaini Ibrahim, Funtua
Zaben fidda gwani na jamiyyar PDP a mazabar Dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Katsina ta kudu, Dakta Shehu Abubakar Matazu ya lashe zaben Sanata da aka gudanar da shi a Hedikwatar mazabar da ke cikin Karamar Hukumar Funtua.
Jami'in gudanar da zaben fidda gwani, Tanimu Audi ya bayyana haka a alokacin da ya ke bayyana sakamakon zaben a Funtua.
Tanimu Audi ya bayyana cewa, Mutane biyu ne suka tsaya takara fidda gwanin, wanda suka hada, Sani Anani Malunfashi da Dakta Shehu Garba Matazu.
"Jami'in ya bayyana sakamkon zaben kamar haka, Sani Anani Malunfashi ya samu kuri'a tamanin da shida sai kuma Dakta Shehu Matazu ya samu kuri'a dari biyu da sitin da bakwai, dan haka Dakta Matazu ya samu nasara zamowa dan takara kujerar Dan Majalisar Datawa na jamiyyar PDP a mazabar Katsina ta kudu. a zaben da za'agudar shekara ta 2023.inji Tanimu Audi.
A nasa jawabin, Dakta Shehu Matazu ya bayyana godiyar sa ga Allah akan nasara da ya samu da kuma Daliget da suka ga cancantars na ya zamo dan takarar su. Insha Allah zamuyi iyaka kokarin na ganin mun kara samun karbuwa ga al'umar yankin Katsina ta kudu dan samun nasara a babban zabe Mai zuwa.
Mazabar Katsina ta kudu ta hada da Kanan hukumomin, Funtua, Faskari, Sabuwa, Dandume, Bakori, Danja, Kankara, Malunfashi, Kafur, Musawa da Matazu.
No comments